Aikin tashar sauke kayan teku a Kano ya kai kashi 80%

Daga WAKILINMU

A halin da ake ciki, aikin tashar sauke kayan teku da ke Kano, wanda Gwamnatin Shugaba Buhari ke gudanarwa ya kai kashi 80 cikin 100 da kammaluwa.

Bayanin hakan ya fito ne daga tawagar duba aikin a ƙarƙashin jagorancin Ministan Sufuri, Rt. Hon. Rotimin Amaechi, ranar Asabar, 5 ga Maris, 2022, inda tawagar ta jaddada cewa wannan tashar mai suna Dala za a sanya a jerin matsayi irin na kowacce tashar jirgin ruwa, idan an kammala ta.

Gina wannan tashar zai dawo da martabar Kano a matsayin Babbar Cibiyar Kasuwanci a Arewa da ma Yankin Afrika ta Yamma bakiɗaya, inda hakan zai buɗe ƙofar samar da ɗimbin guraben ayyukan yi da sana’o’i daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *