Attajirin Saudiyya ya taya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea kan Yuro Biliyan 2.7

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da ƙasar Ingila take tsaka da ɗaukar matakan ladabtarwa ga attajirin biloniyan nan ɗan ƙasar Rasha, Roman Abramovich kuma ƙungiyar ƙwallo ta Chelsea, wacce mallakinsa ce ta shiga cikin halan-halahu. Wato gwamnatin ƙasar ta saka shi a kasuwa tana so ta sayar da shi nan ba da daɗewa ba.

Kodayake, a kwanankin baya da attajirin ya yi niyyar sayar da shi, an ji gwamnatin ta tsayar da tallan ƙungiyar a yayin da take gabatar da matakan ladabtarwa ga shi Abramovich ɗin. Amma a halin yanzu ana tsammanin gwamnatin ta shirya tsaf, don cefanar da ƙungiyar wacce take a birnin Landan, kamar yadda wata majiya ta rawaito cewa, attajirin Mohamed Alkhereji a ƙarƙashin wata tawaga ya yi nufin sayen ƙungiyar a kan Yuro 2.7 wato kwatankwacin dalar Amurka bilyan 3.5 matuƙar an sallama masa.

Mohamed Alkhereji masoyin ƙungiyar Chelsea ɗin ne, kuma shugaban wani kamfanin watsa labarai ne a ƙasar Saudiyya amma ba shi da wata alaƙa ta kai-tsaye da gwamnati. 

Rahotanni daga jaridar Nairametrics sun bayyana cewa, Alkhereiji ya samu goyon baya (ba na kuɗi ba) daga Mohammed bin Khalid Al Saud. Khalid wani jigo ne daga jiga-jigan kanfanin sadarwa na Saudi Telecom Company (STC). Wanda kamfanin sadarwa ne na gwamnatin Sa’udiyya. 

A yanzu haka ƙasar Sa’udiyya ta sanya ranar 18 ga watan Maris ta zama damar ƙarahe ƙarshe da aka ba masu biɗar Chelsea dama su kammala tayin nasu.
 
Mohamed Alkhereiji dai ɗan kasuwa ne mamallakin kamfanin watsa labarai na,  Saudi Media Group, sannan shugaba a kamfanin Mahaifinsa, Abdulelah Alkhereiji, wato Engineer Holding Group. Haka shugaban zartawa a kamfanin talabijin na MBC masu gudanar da tashoshin MBC, da sauransu.

Sannan kuma tsohon ma’aikacin banki ne a Landan, kuma masoyin ga ni kashe ni ne ga ƙungiyar Chelsea ɗin.