Ricikin basasar APC:Yadda Buhari ya ƙwaci Buni daga hannun gwamnoni

*Buni ya yi amai ya lashe kan hukunce-hukuncen Gwamna Bello

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Daga dukkan alamu Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya taka wata muhimmiyar rawa wajen ƙwato jam’iyyar APC daga hannun wasu daga cikin gwamnnoninta kuma ya saka damƙa ta a hannun halastaccen Shugaban Riƙo na Jam’iyyar, Mai Mala Buni, bayan da Shugaban Ƙasar ya ƙi goyuwa da bayan juyin mulkin da aka shirya wa Gwamnan na Jihar Yobe.

Idan za a iya tunawa, a makonnin biyu da suka gabata a ka ji kuma a ka yarda da cewa, Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta shiga rikicin cikin gida na basasa mai alaƙa da shugabanci da kuma babban taron da jam’iyyar za ta gudanar a birnin tarayya Abuja, ranar 26 ga Maris, 2022.

An hango yadda Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ayyana kan sa a matsayin shugaban riƙon jam’iyyar APC a wani taron rantsar da shugabannin kwamitin riƙo na babban taron da jam’iyyar za ta yi. 

Gwamnonin APC akasari sun mara masa baya, kuma sun zargi Buni da ƙoƙarin yi wa APC ƙafar-ungulu, ta yadda taron gangamin jam’iyya na ranar 26 ga Maris a Abuja ba zai yiwu ba.

Shi kuwa Buhari, ya gargaɗe su cewa ahir, kuma su bi hankali, kada garin gyaran doro su karya ƙugu, ko gadon baya baki ɗaya.

Lamarin da ya tayar da hazon siyasar APC da jefa masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar cikin ruɗani, inda aka shiga raɗe-raɗin an yi wa Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Riƙon Jam’iyyar, Alhaji Mai Mala Buni, juyin mulki yayin da ya tafi Dubai, domin duba lafiyarsa.

Haka zalika, wannan lamari ya haddasa musayar yawo tsakanin Gwamna Nasir el-Rufa na Jihar Kaduna da shi Bunin, inda Gwamna na Kaduna ya bayyana cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da damar tsige Buni daga kujerarsa ta shugabancin APC, kuma gwamnoni 19 na jam’iyyar suka goyi bayan haka. Kana el-Rufa’i ya ce, Buni ba zai sake dawowa a matsayin shugaban APC ba har abada.

Shi kuwa Gwamna Buni ya ƙaryata zancen ne, ya na mai mayar da martani da cewa, shine ya sauka da kansa, don zuwa neman lafiya a Dubai, kuma ya miƙa ragamar jam’iyyar a hannun Gwamnan Jihar Neja, Sani Bello.

Ana tsaka da wannan cakwakiya, sai aka ga ɓullar wasiƙar Shugaba Buhari ga Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Sanata Abubakar Bagudu na Kebbi, kuma yana gargaɗin su cewa kada su kuskura su cire Buni kan karagar shugabancin riƙon APC.

A cikin wasiƙar, Buhari ya zayyana masu kuma ya nuna masu alƙiblar da jam’iyyar za ta bi, domin tsallake siraɗin rikicin shugabancin da ya yi mata tarnaƙi da dabaibayi.

Shugaba Buhari a cikin wasiƙar yana cewa, “na fahimci cewa a yanzu haka APC na fuskantar shari’u da dama na rikice-rikice a kotuna daban-daban. Dalilin haka APC na fuskantar barazanar tsoron kada kotu ta soke duk wasu zaɓuka da ta shiga wanda INEC ta shirya.”

Buhari ya ƙara da nuna damuwar yadda APC ta ƙasa shirya taron gangami da wuri tun kafin wuri ya ƙure.

“Ba shakka waɗannan rigingimu da zaman zullumin rashin tabbas na jiran sakamakon hukuncin shari’un da ake yi a kotu, sun zama barazana sosai ga APC. Kuma hakan na iya kai INEC ga haramta duk wasu zaɓuka da APC ta shiga ko za ta shiga tun daga farkon rikicin shugabancin nan. Kai INEC ma za ta iya cewa ba ta san da APC ba a duniya,” inji shi.

Haka wannan gargaɗi ya ke a cikin wasiƙar da Buhari ya aiko wa Bagudu daga Landan a ranar Laraba 16 ga Maris.

Daga nan kuma Buhari ya bayar da umarni uku kan batun shugabancin jam’iyyar kafin zaɓen shugaba da za a yi a ranar 26 ga Maris. Buhari ya ce, a mayar da shugabannin riƙon da gwamnonin APC suka yi wa juyin mulki a kan muƙamansu. Ya gargaɗi gwamnonin APC da magoya bayan su cewa kada su kuskura su sake yin wani katsalandan ko shirmen da zai ƙara hargitsa APC.

“Na ukun kuma shi ne a bar Kwamitin Shugabancin Mai Mala Buni su cigaba da tsarawa da gudanar da Babban Gangamin APC na Ƙasa, wanda za a yi a ranar 26 ga Maris,” kamar yadda wasiƙar ta ƙunsa.

A ƙarshen makon na jiya ne Buhari ya gargaɗi jiga-jigan APC cewa, kada su bari APC ta afka cikin rikicin da ya fi na PDP muni.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa uwar jam’iyya mai mulki APC wasiƙar gargaɗi da jan hankalin yin kaffa-kaffa, kada jam’iyyar ta yi tashin gishirin andurus. Buhari ya yi gargaɗin ne biyo bayan yadda APC ta rikice kuma ta hargitse, yayin da zaɓen 2023 ke ƙara kusantowa. Ya ce, idan su ka bari rikici ya ci ƙarfin APC, to jam’iyyar ka iya ɓalɓalcewa kamar irin ɓalɓalcewar da PDP ta yi, har ta rasa mulki cikin 2015.

PDP ta yi mulki daga 1999 a jere, har zuwa 2015, inda rikici ya dabaibaye ta, APC ta ƙwace mulki a hannun ta, bayan ta shafe shekaru 16 ta na mulki.

Yanzu kuma rikici ya cukuikuye jam’iyyar APC tun ba ta ma cika shekaru 7 kan mulki ba, kuma yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa.

Sai dai kuma da ƙarshe, Mai Mala Buni ya yi fatali da raɗe-raɗin warware duk ayyukan da shugaban riƙo, Gwamna Bello ya aiwatar a lokacin da ba ya ƙasar. Buni ya musanta soke ƙananan kwamitoci da Gwamnan Neja ya kafa lokacin da yake Dubai, ya amince da ayyukan baki ɗaya.

Sai dai har yanzun babu cikakken bayani ko amincewar da Buni ya yi wa ayyukan Bello, har da tsige sakataren CECPC, Sanata John James Akpanudoedehe. Wannan matakin ba ya rasa nasaba da dabarun ɓangaren Buni na sansatawa da mambobin CECPC da ke ganin an musu ba daidai ba.

A ranar Alhamis da ta shuɗe, Buni ya rushe dukkan jerin ƙananan kwamitoci da gwamnan Neja ya kafa domin taimaka wa wajen shirya babban taro na ƙasa. A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren APC na ƙasa, Buni ya zare sunayen mambobin CECPC daga kwamitocin, inda ya bar kansa da sakatare kaɗai. Sai dai hakan bai yi wa ɓangaren Gwamna Bello daɗi ba, nan take suka fitar da bayanin cewa sun amince da tsige Sanata James Akpanudoedehe daga matsayin sakatare.

A wata sanarwa da ya sa wa hannu da kansa, Buni ya ce ya miƙa ragamar jagoranci hannun Gwamna Bello kafin tafiyarsa, don haka duk matakan da ya ɗauka suna kan doka.

“Mu na mai sanar wa masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar cewa zancen soke duk ayyukan da shugaban riƙo, Gwamna Bello na jihar Neja ba gaskiya ba ne. Saboda haka, duk ayyukan da aka aiwatar lokacin da bana ƙasa suna nan daram kuma a kan doka. Muna shawartan masu faɗa aji da mambobin jam’iyya su yi fatali da jawabin baya da ya soke ayyukan shugaban riƙo.

“Idan ba ku manta ba na miqa ragamar jagorancin APC a hannun maigirma Gwamnan Neja, Abubakar Bello, domin tafiya duba lafiya. Bisa haka, duk matakan da ya zartar a wannan lokacin suna nan,” inji Buni.