Matar Marigayi Ojukwu da ta gwamnan Anambara mai barin gado sun tsinke juna da mari a taro

Daga AISHA ASAS a Abuja
 
Kallo ne ya koma sama a wajen rantsar da Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuka Soludo, a jiya Alhamis, bayan da matar gwamna mai barin gado, Obelechukwu Willie Obiano, ta tsinka wa Bianca Ojukwu mari a bainar jama’a, inda nan take faɗa ya kaure a tsakaninsu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan da gwamnan mai jiran gado, Farfesa Soludo, ya ɗauki rantsuwar kama aiki.

Kamfanun NAN ya ruwaito cewa, manyan baƙi su na zazzaune lokacin da mai-ɗakin Obiano ta iso.

Tana shigowa, ta na taku ɗaiɗai sai ta nufi sahun gaba inda maiɗakin Ojukwu ke zaune, inda bayan ‘yar musanyar yawu, sai ji aka yi tas!, wato ta kashe ta da tafi.

Lamarin ya ja hankalin jami’an tsaro da kuma sauran manyan baqi, waɗanda su ka yi maza su ka janye matar Obiano daga kan Bianca, wacce aka hango ta cika da mamaki.
Daga nan ne sai aka fice da matar Obiano daga wajen taron, inda daga bisani mijin nata ya bi bayan ta, bayan an rantsar da sabon gwamna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *