NAPTIP ta ceto ƙananan yara 30 daga hannun miyagu cikin shekara guda

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane na Ƙasa (NAPTIP), ta umurci duka shiyyoyin ta dake duka jihohin ƙasar nan da su fara gudanar da sintiri na musamman cikin gaggawa a yankunan su don tabbatar an cafke duka waɗanda ke safarar yara ƙanana, ciki har da waɗanda ke da hannu cikin harkokin saya da sayar da mutane don su fuskanci hukuncin doka. 

Darakta Janar ta hukumar, Dr. Fatima Warizi-Ari ce ta ba da umurnin a cikin wata takardar jawabin harkokin hukumar cikin shekara ɗaya, wanda daraktar ta sanya hannu sa’anan mai magana da yawun hukumar Misis Stella Nezan ta bai wa wakilin mu kwafi a hedikwatar hukumar dake birnin tarayya Abuja ranar Litinin 14 ga watan Maris na shekarar 2022 da ake ciki.

Daraktar ta bayyana a takardar cewa aƙalla kimanin yara ƙanana 30 ne hukumar ta ceto daga hannun waɗannan miyagun mutane dake safarar yara a cikin shekara guda da ta gabata. 

Akan haka ne ma ya sa hukumar ba ta yi wata-wata ba, inda ta umurci a gudanar da sintirin musamman a duka gidaje da ake zaton ana saya da sayar da yara don a gano tare da hukunta masu harkar. 

Ta buƙaci duka shiyyoyin hukumar na jihohi su haɗa kai da sauran hukumomin tsaro dake yankunan su don gudanar da sintirin haɗin kai don taka wa miyagun mutanen birki. 

Daraktar wace ta kuma tavo wani mummunar lamarin nan da a cewarta ya auku kwanakin baya, inda wani ya sato wani qaramin yaro ya ɓoye shi a akwati ya ɗaura a keken sa da sunan zai kai wa wani saƙo kafin jami’an tsaro suka cafko shi. 

Ta ce bai kamata a bari irin wannan abu yana cigaba da faruwa a ƙasar nan ba. Ta kuma yi amfani da damar inda ta bayyana cewa ta tabbata jami’an ‘yan sanda za su kwatanta adalci a shari’ar sace yaron kuma za su bayyana gaskiyar lamarin a ƙarshe.

Ta cigaba da bayyana cewa “ba za mu cigaba da zura ido muna kallon irin waɗannan ayyukan ta’asa na ci gaba da gudana a ƙasar nan ba. Kundin tsarin dokar safarar mutane na shekarar 2015 ta ba mu dama da ikon yaƙi tare da hukunta duka laifuffukan ciki har da na saya da sayar da mutane da kuma cin zarafin yara ƙanana da sauransu. Misali kowa ya san mummunar niyyar wannan wanda aka kama ɗauke da yaro cikin akwati a keke da kuma waɗanda suka turo shi? Wa ya kuma san hali da mahaifiyar yaron ke ciki a yanzu sakamakon aukuwar lamarin?. 

“Kamar yadda na sanar a cikin shekara guda kacal da ta gabata wato 2021 hukumar nan ta ceto kimanin ƙananan yara 30 daga waɗannan miyagun mutane a sassa daban-daban na ƙasar nan baki ɗaya, inda muka kuma nemo iyayen su muka haɗa su da su. Yayin da su kuma Waɗanda muka cafken suna fuskantar hukunci daban-daban daidai da laifin da suka aikata,” inji ta.