Waye shugaban jam’iyyar APC?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Har dai ka ga shugaba Buhari ya fitar da sanarwa musamman a kan lamarin jam’iyya to yanayin ya kai matuƙar rikicewa. Sanarwar ta bayyana ne alhali shugaban na Landan don ganin likita. A gaskiya duk mai bin tsarin shugaban tsawon shekaru zai fahimci ba kasafai ya kan sa baki ko ya tsawata in ’yan jam’iyya na ɗauki ba daɗi da juna ba. In ka ɗebe lokacin tsayawa takarar sa ko abubuwan da su ka shafe shi, ba ya sa bakinsa a harkokin jam’iyya.

Akwai lokacin da wasu su ka kanbama cewa shugaba Buhari ne ya yi jam’iyyar ba ita ta yi shi ba. Ma’ana kasancewarsa a jam’iyya ya sa ta zama mai tasiri har da ta kan samu miliyoyin ƙuri’u a zave. A duk lokacin da shugaba Buhari ya tsaya takara tun daga 2003, a kan alaƙanta ƙuri’un da ya samu ne da shi ba da albarkacin jam’iyya ba. Bayan zaɓen 2007, shugaba Buhari a lokacin ya na jam’iyya ANPP sai a ka ayyana marigayi shugaba Umaru Musa ’Yar’adua a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a tutar PDP.

Shugaba Buhari ya yi niyyar tafiya kotu, amma sai jam’iyyar ta yi tutsu ta nuna ba ta aniyar tafiya kotun. Sai ya zama marigayi ’Yar’adua ya ce zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. Wannan ya ba da dama ya naɗa kimanin mutum 5 na ANPP a muƙaman gwamnatinsa ciki kuwa har da marigayi tsohon sakataren jam’iyyar Garkuwan Gombe Sanata Sa’idu Umar Kumo. Matsayar ANPP ba ta yi wa shugaba Buhari da magoya bayan sa daɗi ba, don haka sai ya cigaba da ƙararsa shi kaɗai har a ka je kotun ƙoli. Marigayi babban alƙali Idris Legbo Kutigi ne lokacin babban alƙalin.

Bari na ba da wani labari da ba a tantance sahihancinsa ba a kan Kutigi. An ce an zo za a gina ma sa gida ya zaɓi inda ya ke son ginin, sai ya ɗauki masu niyyar ginin ya nufi maƙabarta da su ya nuna mu su inda ya kamata a gina ma sa gidan don wannan shi ne gidan gaskiya. Da haka maganar gina gida ta mutu. Da wannan labari da ya zama kamar labarun da da na yanzu magoya bayan shugaba Buhari su ka samu kwarin gwiwa cewa kotu za ta ba wa Buhari nasara. A ranar yanke hukunci sai a ka samu canjaras inda alƙalai 3 su ka soke zaven marigayi ’Yar’adua su ka ba wa hukumar zave kwana 90 ta shirya sabon zaɓe.

A gefe guda alƙalai 3 su kuma su ka ce zaɓen ’Yar’adua ya yi daidai. A wannan yanayi ya nuna saura mai raba gardama wato babban alƙali ya yanke na sa hukuncin tsakanin goyon bayan masu soke zaɓe ko mara baya ga ɓangaren masu hukuncin zaven ya yi daidai. A ’yan kalmomi kaɗan a Turance marigayi Idris Kutigi ya ce, “THE PETITION IS HEREBY DISMISSED” wato ma’ana an kori ƙarar da shugaba Buhari ya shigar! Daga nan ba sai na ce tunanin waliyantakar shari’a da a baya wasu su ka ɗauka Kutigi na da ita ta faɗa kwandon shara ba.

Bayan zaɓen 2007 da yanke wannan shari’a, sai shugaba Buhari da muƙarrabansa su ka fara shirin kafa sabuwar jam’iyya wacce kuma haka lamarin ya kasance a ka kafa CPC da shugaban ya yi takara a inuwar ta a 2011. Bayan fitowar sakamakon zave da hukumar zaɓe INEC ta ayyana tsohon shugaba Goddluck Jonathan na PDP ya lashe, sai rashin jituwar ɗalilan rashin nasarar CPC musamman a jihohi ya yi yawa.

An yi amanna cewa CPC za ta lashe Katsina, Kano, Bauchi da sauran su. Ƙarshe dai CPC jihar Nassarawa ta lashe da ƙyar da jibin goshi ta hanyar tsohon gwamna Tanko Almakura wanda shi ma bata ma sa rai da a ka yi a PDP ya sa shi rungumar APC da ɗaukar Solomon Ewuga ya yi ma sa mataimaki.

Zarge-zargen sun nuna an sauya sunayen ’yan takara kamar a Katsina an ki amincewa da Lado Danmarke ya yi takarar sai a ka miƙa tikiti ga gwamnan jihar na yanzu Aminu Bello Masari wanda tsohon gwamna Ibrahim Shema ya yi nasara a kansa.

Kafin zaɓen an ruwaito wasu majiyoyi masu nuna har Shema ya fara tattara kayansa don ficewa daga Katsina amma tun da a ka sauya ɗan takara sai hankalinsa ya kwanta. Haka a Kano Muhammad Abacha ya samu takarar maimakon Lawan Jafar Isa.

A Bauchi Danchaina ya rasa Yusuf Maitama Tuggar ya samu. An aza laifin kan Injiniya Buba Galadima wanda a lokacin ya na sakataren CPC. Amsar da Galadima ya kan bayar ita ce duk wanda ya sauya sunansa da umurnin shugaba Buhari ne, don haka duk mai ƙalubalantar sa ya je ya ƙalubalanci Buhari. Ma’ana ba shi ya kar zomon ba, rataya a ka ba shi.

Na halarci wani taro a LAGOS HALL na masaukin baƙi na Hilton inda ’yan CPC su ka yi dafifi su na son sasanta kan su bayan rashin nasarar zaɓe. Shugaba Buhari ya na sauraron su, su ka amayar da duk abun da ya ke damun su. A na ta ƙus-ƙus cewa yau shugaba Buhari zai yi fyaɗar ’ya’yan kaɗanya, zai shiga tsakani ta hanyar ba wa marar gaskiya rashin gaskiyar sa. Ya zo jawabi a na ta fatar cewa zai yi magana mai muhimmanci ta manyan ’yan siyasa ko jagorori, amma sam ba haka lamarin ya auku ba. Budar bakinsa ya ce ta yaya zai tsawata mu su alhali su na ta faɗa wannan ya kai wancan ƙara kotu. Don haka bayanin na sa na nuna duk abun da su ka ga dama su yi ta yi shi ba abin da zai ce mu su. Jikin su ya yi sanyi don jagoran su ya gwale su.

A baya-bayan nan ma za a tuna yadda tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu saɓani da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Mutane sun yi ta sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai tsawata wa sassan biyu, don su yi sulhu a tsakaninsu, amma ƙarshe dai sai da su ka raba gari. Ba ma kan lamarin siyasa ba, in za a tuna rashin fahimta ko saɓani tsakanin Sarki Muhammadu II da Gwamna Ganduje ya kai matsayin har kwamitrin dattawa a ka samu da su ka je Kano don sulhunta sassan biyu. Mutane sun yi ta sa ran shugaba Buhari zai shiga tsakani don a kashe wutar, amma hakan bai yiwu ba har ta kai ga kwave sarkin da tura shi hijira a wani ƙauyen Jihar Nasarawa mai suna Loko.

Hatta a fadar Aso Rock an samu saɓani tsakanin uwargidan shugaban Aisha da ’yan uwan shugaban. In ma dai an samu sulhu a bayan fage ba za mu iya sani ba, amma abun da ya fito fili an yi ta kai ruwa rana inda Hajiya Aisha ta riƙa furta kalamai. An ji a wani faifan bidiyo inda ta ke furta kalmomi masu zafi ga wata mata a fadar kan buɗewa ko rufe wata ƙofa.

Allah ya sa daga bisani bayan faifan ya yaɗu a duniya Hajiya Aisha ta yi nazarin ran mutane zai sosu game da haka don haka ne ma ta ba da haƙuri. Ko a gwamnatance an sha shan mamakin shugaban ya tura sunan Ibrahim Magu don a tantance shi a majalisar dattawa ya zama shugaban hukumar yaƙi da cin hanci EFCC.

Kwatsam sai a samu umarni ko saƙo daga wata hukumar tsaro cewa ya na da aibu kaza da kaza don haka bai cancanci a naɗa shi wannan mukami ba. Da yawa an ɗauka za a ga bacin ran shugaba Buhari cewa ya tura sunan mutum amma wani ya kawo cikas kuma ya na cikin gwamnatin sa!

Yanzu ga wannan damvarwar ta APC inda a ka yaɗa labarin cewa shugaba Buhari ya yi umurnin a kwave gwamna Mai Mala Buni daga jagorancin kwamitin shirya babban taro da naɗa gwamna Abubakar Sani Bello. Ba takarda ko bayani na baki. Gwamna Nasiru Elrufai ne ya fito karara ya ce shugaban ne ya ce a kwave Buni. A na su ɓangaren jami’an cikin jam’iyyar sun ce sam ba su san da wannan maganar ba. Shi ma Gwamna Sani Bello bai yi wani bayani filla-filla mai nuna an naɗa shi don maye gurbin gwamna Buni ba, sai ya ce shi ne a yanzu shugaban kwamitin shirya babban taron.

An ga wasiƙa daga hukumar zaɓe da ke nuna ba ta san maganar sauyin shugabanci a APC ba kuma har dai za a yi ma ta gayyatar zuwa wani taro sai an ba ta sanarwa da tazarar kwana 21 bisa tanadin sabuwar dokar zaɓe.

Haƙiƙa ’yan APC sun samu ajiyar zuciya da su ka ga sanarwa daga shugaba Buhari da ke nuna kowa ya maida wuƙa kube da kuma daina shiga kafafen labaru su na aibanta juna. Shugaban da zai gama wa’adin sa na ƙarshe a ranar 29 ga mayun 2023, ya ce, da irin wannan rashin jituwa PDP ta faɗi zaɓe a 2015.

Shugaban ya buƙaci haɗin kan ’yan jam’iyyar don samun gudanar da babban taro a ranar 26 ga watan nan. Mu dai a nan sai mu ce Allah ya kai mu ranar mu ga abin da zai faru. Allah ya ba wa mai rabo sa’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *