Gwamnatin Katsina ta samu tallafin Dala miliyan takwas don inganta rayuwar mata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta sake samu tallafin Dalar Amurka Miliyan 8 ($8m) daga bankin duniya domin shirin Nigeria for Women.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na faɗaɗa shirin Nigeria for Women (NFWP) zuwa dukkanin ƙananan hukumomi 34 na jihar, bayan da bankin duniya ya amince da bayar da ƙarin tallafin da ya kai tsakanin dala miliyan 6 zuwa miliyan 8 domin aiwatar da shirin a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar jami’ain bankin duniya, ma’aikatar harkokin mata ta tarayya da kuma masu gudanar da Shirin Nigeria for Women a masaukin Gwamnan Jihar Katsina da ke Abuja.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Katsina ta riga ta ware Naira biliyan 4 a matsayin kuɗin tallafin da ake buƙata daga jiha, yana mai jaddada cewa ƙarfafa tattalin arzikin mata na daga cikin manyan hanyoyin rage talauci, bunƙasa tattalin arzikin iyalai da kuma ƙarfafa zaman lafiya a al’umma.

Haka kuma, ya sanar da shirin gwamnatin jihar na ƙaddamar da wani shiri mai suna “Nigeria for Men”, wanda zai mayar da hankali kan bunƙasa sana’o’i, ƙarfafa matasa su dogara da kansu da kuma inganta ci gaban al’umma.

Gwamnan ya yaba wa matan da ke cin gajiyar shirin bisa yadda suka rungumi tsarin, inda ya bayyana cewa sun tara kusan Naira miliyan 192 ta hanyar ajiyar kuɗi kafin samun tallafin shirin, yana mai cewa hakan alama ce ta jajircewa, gaskiya da kuma dogaro da kai.

Tun da farko, ministar harkokin mata ta tarayya, Hajiya Imaan Ibrahim Suleiman, ta bayyana Jihar Katsina a matsayin abin koyi ga sauran jihohin Najeriya wajen aiwatar da shirin Nigeria for Women. Ta sanar da cewa an magance matsalolin da suka jinkirta aiwatar da shirin, tare da tabbatar da cewa za a fitar wa Jihar Katsina tsakanin dala miliyan 6 zuwa miliyan 8 domin faɗaɗa shirin.

Ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin samar da ƙarin dala biliyan ɗaya da rabi domin faɗaɗa shirin zuwa sassan ƙasar baki ɗaya.

Shi ma Shugaban tawagar bankin duniya mai kula da Shirin Nigeria for Women, Mista Micheal Ilesanmi, ya yaba da kyakkyawan jagorancin Gwamna Raɗɗa, yana mai tabbatar da cewa za a fitar da sabon tallafin cikin wannan shekara domin aiwatar da shirin a Katsina.

Ya kuma bayyana cewa ana sa ran mata na farko da suka cika ƙa’idojin shirin za su fara samun damar cin gajiyar shirin (Community Investment Fund) cikin watanni uku masu zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply