Jami’an Hisbah sun ƙwace katan-katan na giya a Kebbi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Jami’an Hukumar Hisbah a jihar Kebbi ranar Asabar da ta gabata ne suka ƙwace katan-katan na nau’in giya daban-daban a Birnin Kebbi, helkwatar jihar.

Ma’aikatan na hisbah waɗanda suka yi amfani da wasu bayanan sirri suka dira wa wani saƙo kusa da tsohuwar kasuwa inda suka riski wata mota an cika ta tab da barasa kuma tana ƙoƙarin zuwa kasuwanci lokacin da suka ritsa ta.

Wannan dabara ta yin kasuwancin giya, kamar yadda kwamandan hisbah na jihar ya bayyana, ya yi bambaraƙwai da dokokin jihar Kebbi waɗanda suka hana fatauci da shan barasa a ɗaukacin faɗin jihar, in bacin barikin soji da makamantan wurare.

Kwamandan Hisbah na jihar ta Kebbi, Alhaji Suleiman Mohammed, wanda ya yi wa manema labarai a farfajiyar kamen, ya ce hukumar su za ta cigaba da yin irin wannan samame da zummar dokar da ta hana sha da safarar barasa a jihar, har zuwa lokacin da masu shanta za su daddara da yin ta’ammali da barasa.

Ya bayyana cewar, hukumar hisbah za ta faɗaɗa bincike kan wannan lamari kafin a ɗauki matakin doka bisa wannan kame.

Mohammed, sai ya yi kira ga masu kunnen ƙashi na rashin bin doka, waɗanda ke danganta wannan hali nasu da ammashuwa, da yi wa doka karan-tsaye, da su guji aikata ire-iren waɗannan munanan ayyuka domin amfanin kan su.

Duk ƙoƙarin da manema labarai suka yi domin ji daga bakin wanda ya mallaki barasar, lamarin ya ci tura saboda ya gudu.