Majalisa tana bibiyar kamfanonin mai 77 kan rashin biyan haraji

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Talatar da ta gabata ne dai majalisar Wakilan Nijeriya ta cigaba da sauraron wani jawabi a game da bincike game da bashin Naira Tiriliyan 2.6tn da gwamanatin tarayya take bin kamfanonin mai guda 77 a Nijeriya. 

Majalisar tana gudanar da wannan bin diddigi ne da dogaro da rahoton da aka samar a kan kamfanonin da suka shafi albarkatun ƙasa a shekarar 2019.

Kakakin Majalisar Wakilan, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa, in dai kamfanonin da ake bin bashin ba za su ba da haɗin kai ba, to kuwa za su tilasta wa majalisar ɗaukan mataki a kan duk kamfanin da ya yi buris. Kuma a cewar sa, majalisar za ta fara bibiyar duk waɗannan kamfanoni don tabbatar da sun biya bashin. 

Gbajabiamila ya qara da cewa, Naira tiriliyan 2.6tn  ba fa kuɗi ne na wasa ba da za a ce wai a bar shi ya bi ruwa ba. Musamman a wannan lokaci da gwamnatin Tarayya take fama da ƙarancin kuɗaɗen haraji don ɗaukar nauyin kasafinta na shekara-shekara.

Kakakin majalisar ya ƙara da cewa: “Ina so mutane su fahimci irin muhimmancin da yake cikin aikin bibiyar amsar harajin da za mu fara, bari na yi bayani ɓaro-ɓaro, in dai aka samu wasu kamfanoni ko wasu mutane da suka qi ba da haɗin kai ga kwamitin a yayin aikin(amsar harajin), Zan yi abinda ba a taɓa yi a tarihin wannan majalisar ko na Duniya ma bakiɗaya ba, wato da kaina zan ƙaddamar da hukunci a kansa na sa hukuma ta kama shi kamar yadda tanadin kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada (ga mai laifi irin nasa). Wannan shi ne irin muhimmancin da aikin yake da shi.”

A cewar sa, akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin tattara haraji da kuma ayyukan gina ƙasa. Dukka suna da matuƙar muhimmanci shi ya sa majalisar ta yi wannan hangen nesa suka haɗa wannan kwamiti na musamman duk da dama akwai kwamitin da yake tsaye yake duba wannan sha’anin. Kuma cewar sa ya san za a yi aiki tuƙuru kuma a samu sakamakon da ya kamata.  

Haka zalika, Gbajabiamila ya bayyana babban dalilin da ya sa majalisar wakilan ta yanke shawarar yin wannan binciken waɗancan basussukan shi ne, domin a warware matslar wannan bashi da yake tsakanin gwamnatin Tarayya da kuma waɗancan kamfanonin man. Kuma ya ƙara da cewa, Naira Tiriliyan 2.6tn ba ƙaramin kuɗi ba ne musamman a halin yanzu da ƙasar Nijeriya take fuskantar ƙalubale a kan rashin haraji don haka, dole gwamnati ta yi iya ƙoƙarinta don ganin ta lalubo duk wasu maƙalallun kuɗaɗenta don warware matsalolinta. 

Shi ma shugaban kwamitin kuma mataimakin bulaliyar majalisar, Nkeiruka Onyejeocha ya bayyana cewa, a yayin da gwamnatin tarayya take tsananin buqatar kuɗaɗe domin ta ɗauki nauyin kasafinta na shekarar 2022, su kuma kamfanonin man fetur ɗin sun ƙanƙame mata kuɗaɗenta. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *