Mun kashe Naira tiriliyan 1.3 cikin shekaru biyar don inganta lantarki, cewar Gwamnan CBN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cikin halin ƙuncin rashin wutar lantarki, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa a cikin mulkin Buhari bankin ya kashe Naira tiriliyan 1.3 wajen qoqarin ganin an bunƙasa kuma an inganta wutar lantarki a faɗin ƙasar nan.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, a ranar Litinin.

Wannan bayani na sa ya zo ne kwana kaɗan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya haƙuri saboda gagarimar matsalar wuta da ake fama da ita a ƙasar nan, tun a farkon watan Fabrairu.

Emefiele ya yi wannan sanarwa a ranar da Buhari ya kira Ministan Makamashi Abubakar Aliyu domin jin halin da ake ciki dangane da matsalar wutar lantarki.

A yanzu haka tashoshin samar da wuta 14 duk sun durƙushe, lamarin da ya jefa Nijeriya cikin duhu.

Sai dai kuma abin mamaki shi ne irin adadin maqudan kuɗaɗen da CBN ya kashe a cikin shekaru biyar na mulkin Buhari, zai ba jama’a da dama mamaki.

Emefiele ya ce CBN ya kashe Naira tiriliyan 1.3 ta fannoni daban-daban don inganta wutar lantarki a Nijeriya, a cikin shekaru biyar da suka gabata.

“Mun kashe Naira Tiriliyan 1.3 cikin shekaru biyar, ko dai ta hanyar sayen manyan janareto na wuta, raba kuɗaɗe ga kamfanonin saida wuta, ‘Discos’, ko ta dalilin sayo kayan injina da kayan gyara, ko sayen mita, ko kuma ƙarin kuɗaɗe ga kamfanonin samar da wuta.

Idan za a iya tunawa ƙungiyar SERAP ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya sa Ministan Shari’a Abubakar Malami da EFCC da ICPC su binciki masu hannu wajen kashe aƙalla Naira tiriliyan 11 a ɓangaren gyaran wutar lantarki, tun daga 1999 har zuwa yau.

SERAP ta ce ba zai yiwu ƙasa kamar Nijeriya ta riƙa kasancewa cikin duhu ba, amma a duk shekara wasu na danne biliyoyin nairorin da ake warewa da sunan gyaran matsalar wutar lantarki.

Wannan kira na SERAP ya zo ne daidai lokacin da Nijeriya ke cikin wata gagarimar matsalar wutar lantarki, inda yawan wanda ake samu bai wuce mega wats 2200 ba.

SERAP ta ce daga 1999 zuwa yau, an ragargaje zai kai Naira tiriliyan 11, wuta ba ta gyaru ba, sannan babu kuɗaɗen babu alamar su, an yi biyu-babu kenan.

Kan haka ne SERAP ta ce a gaggauta yin bincike, a kamo, a gurfanar kuma a ɗaure duk wanda aka samu da laifin karkatar da kuɗaɗen aikin gyaran wuta ko wane ne. Sannan kuma a taka cikin sa sai ya amayar da kuɗaɗen da ya karkatar.

Wannan wasiƙa dai SERAP ta aika wa Buhari ita a ranar 19 ga Maris 2022, mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare.

“An shafe shekaru masu ‘yawa ana yi mana ‘yar-burum-burum kan aikin gyaran wutar lantarki a ƙasar nan.

“SERAP na tunatar da Buhari cewa sai ka cika alƙawarin da ka ɗauka a ranar rantsar da kai, 29 ga Mayu, 2015, sannan wuta za ta gyaru.

“Babban abin kunya ne a ce kamar Nijeriya ƙasa mai sama da mutum miliyan 180 amma ba su iya samun wutar da ta wuce miga wats 4000.

“Ba za mu tava barin haka ya ci gaba ba,” inji Buhari a cikin jawabin sa a 2015.

Sannan kuma SERAP ta nemi Buhari ya bi umarnin kotu wanda Mai Shari’a Austine Chuke Obiozor ya umarci Gwamnantin Tarayya tun a cikin 2019 cewa ta fallasa sunayen Waɗanda su ka ci kuɗaɗen gyaran wutar lantarki, sunayen kamfanoni da adadin kuɗin da kowa ya salwantar.