Auren talaka ko mai arziki ko kuma ƙwarya ta bi ƙwarya (2)

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkan mu da sake haɗuwa a wani makon a filinku na Zamantakewa daga jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu cigaba daga inda muka tsaya a makon jiya. Wato samar da zaɓi tsakanin auren talaka, ko mai kuɗi ko kuma ƙwarya ta bi ƙwarya. A inda muka yi bayani sosai a kan illolin auren namiji mai arziki ga macen da ta fito daga gidan talauci. Duk da dai akwai ribobi kamar za ta samu jin daɗin rayuwa kuma ta fita daga ƙangin talauci da babu da sauransu. Sai dai kuma yana tattare da wasu ƙalubale. A wannan mako kuma za mu kawo yadda auren talaka yake ga mace wacce ta fito daga gidan wadata. Sai ku biyo mu don jin yadda za ta kaya. 

Aure kamar yadda na faɗa a baya kamar haɓo ne. Sannan samun abokin rayuwa kamar ƙaddara ce wacce bawa bai isa ya guje mata ba. Domin wani ba ya auren matar wani ko wata ta auri mijin wata. Sai dai aure tsakanin diyar masu wadata da talaka wani abu ne da yake nuna tsantsar tsagwaron tasirin soyayya. Duk yadda aka san mace da son ƙyale-ƙyale da son gidan hutu amma ta zaɓi talakan miji don ƙarashe rayuwarta tare da shi. Hakan yana daga cikin kyawawan abubuwan da suke faruwa a rayuwar Duniya. Sai dai kamar yadda aka ce rayuwa tamkar sha ne daga kuttun zuma ne da maɗaci. Don haka, akwai wasu ƙalubale da ba a rasa ba. Wasu daga ƙalubalen ‘yar masu wadata ta auri talaka sun haɗa da:

*Juyin rayuwa: Babban ƙalubalenta shi ne sauyin rayuwa. Zaɓin da kika yi na mijin aure dole sadaukarwa kika yi ga barin rayuwar jin daɗi da daular da kike ciki i zuwa rayuwa wacce ba ki saba ba. Shin kin shirya wannan sadaukarwar? In dai ba ki shirya yin wannan sadaukarwar ba, to kada ki fara shiga wannan rayuwar. Domin ba abinda za ki tsinta sai nadama. Domin kin saba da samun komai a wadace a gaban iyayenki, yanzu ko dole ki yi haƙuri da sabuwar rayuwa ta wataran akwai wataran babu. Ko kuma ma kullum a babun! Don haka maganin kada a yi, kada a fara! Kuma ki sani, samun namiji shi ne wadatuwarki. Duk yadda iyaye da dangi za su taimaka miki ba zai isa ki yi rayuwar walwala ba matuƙar mijinki ba shi da hali.

*Hassada: Kamar yadda muka sani a ɗabi’ance marasa shi ba su da abokin gabar da ya wuce masu wadata. Musamman masu kuɗin da ba sa taimakawa. Sai dai idan an samu mutanen kirki sosai. Don haka, talaka ke yi musu jam’u a ƙiyayyarsa da yi musu mugun fata a kullum. Da zarar kika aure shi kuwa, nesa ta zo kusa. Ke ma da kika aure shi ba ki da banbanci da sauran masu kuɗin da yake ganin suna da son rai. Don haka, zuciya ba ta da ƙashi ba zai iya danne zuciyarsa a kan yi miki hassada ba. Tun daga kan rayuwar da kika taso ta alfarma, da irin cigaban da kike da shi wanda shi ba shi da shi. Hakazalika danginsa dole su ma za su dinga baƙinciki da samunki. Sai dai idan kin iya dabara sosai wajen nuna rashin girman kai da rashin son abinki tare da nuna rashin ƙyama gare su. 

*Rashin godiya gare ki: Hakazalika ki shirya, ba komai za ki yi mijinki ko yaran miji ko danginsa su gode miki ba. Komai kika yi musu za su raina su dinga ganin ya kamata ki yi musu abinda ya fi haka. Shi kansa mijin zai so ki sakar masa komai naki ba wai ki dinga sam masa ba. Rashin ba shi dukkan dama kan iya jawo muku rikici a cikin lamurranku. 

*Rashin fahimtar juna: Ko da ba ma’aurata ne ba, tsakanin mai wadata da talaka za a samu rashin fahimta wasu lokutan. Musamman saboda banbancin asali. Wanda ba wani abu ne zai jawo haka ba sai zargi da kuma jin kai/ girman kai. Domin ke za ki ga kina da arziki kuma kina ɗauke masa wasu wahalhalun gida, dole ya dinga godewa. Shi kuma zai dinga tsoron nuna miki godiya kada ki ga gazawarsa sannan zai dinga zargin kada ki dinga jin kanki ki ƙi yi masa biyayya saboda kin fi shi arziki da wadata. Zai ta zargin an raina shi da sauransu.  Ga rashin fahimtarki da ganin ana so a mallake shi da dukiya. Abubuwa dai ga su nan. Sai kun yi yaqi da shaiɗan da kuma son zuciya za ku iya kauce wannan fitinar. 

*Dogaro da ke da iyayenki: Akwai mazajen da da ma suna auren ɗiyar masu wadata saboda su huta. Idan aka yi sa’a kina yi masa hidima sosai ko iyayenki na yi masa, hakan zai ƙara kashe masa zuciya. Kuma komai ya sa muku ido ya ki yin komai ko yaransa ma ke ya dogara ki yi komai a gidan. Ko asibiti, ci, sha, duk sai ya ƙi yi ko da yana samun kuɗi. Saboda taƙamar dole sai kun yi. Maslaha dai kada ki sake ki saba masa haka tun farko. A bar shi ya nema da guminsa ya yi. Ke ki zama ‘yar tallafawa kawai. Tallafawar ma idan zai yiwu a ɓoye, ki voye. Don kada ki fiye tallafawar ya ga kamar kina neman gazawarsa. Wasu mazan ko iyayen mace na da wadata ba sa yarda a yi musu komai. Saboda gudun kada zuciyoyinsu su mutu. Shi kuma wanda ya bari zuciyarsa ta mutu, sai dai mace ko iyayenta su yi masa abu, to da ma ya tsammaci wulakanci da gori watarana.  Don da ma ba zancen ganin mutunci tsakaninsa da surukai ko matarsa. 

*Ƙaranta: Dole sai kin kawar da kanki a kan wasu abubuwa na ƙaranta da sa ido. Misali ki ga uwar miji an kawo mata abinci ta lashe a gidan surukai, da sauransu. Ko sa ido da sauransu. 
*Zargin rashin tarbiyya: Kamar yadda mai kuɗi a wajensa talaka ba shi da tarbiyya, haka shi ma talaka a wajensa masu kuɗi ba su da tarbiyya. Ba wani abu ne ba fa illa banbancin asali.

*Samun damar ƙara aure don ba shi da nauyi: Kamar yadda muke gani a ƙasar Hausa, yawanci namiji da zarar ya ji rarar ‘yan canji a hannunsa to fa sai zancen ƙaro aure. Sai dai idan mai tsari ne ko kuma ba shi da ra’ayin tara mata. Yayin da namiji ya auri ‘yar masu wadata wacce komai ta ɗauke masa ko iyayenta sun  ɗauke masa, shikenan sai tunanin ƙaro aure. Don haka ki kwana da sanin haka in dai kika auri wanda kika fi shi wadata. 

Amma kuma fa ba tare aka haɗu aka zamo ɗaya ba. Wani zubin ma namiji mara wadata yana sauƙin kai da fahimta ba kamar mai kuɗi ba musamman idan kika sakar masa komai yana lura da shi. Kuma ba ki ƙasƙantar da shi ba saboda kin fi shi hali ba. 

Kuma ‘yaruwa ki sani, a wannan aure sai kin ɗaura ɗamarar sadaukar da kanki. Da cire girman kai domin a samu daidaito yadda ya kamata. Kuma banda raina danginsa da iyayensa. 

To idan haka ne, ƙwarya ta bi ƙwarya za a yi? 

To ƙwarya ta bi ƙwarya wato dai mai kuɗi ya auri ‘yaruwarsa mai kuɗi, kuma talaka ya auri ‘yaruwarsa talaka. Amfanin haka shi ne, asalinku ɗaya, don haka babu zancen rashin fahimtar juna da zargin rashin tarbiyya. Sannan akwai fahimta sai dai kuma akwai girman kai da ji-ji da kai  tsakanin dangogin guda biyu. Kowa ba zai yarda yau a ce nasa ya yi laifi ko ya tavu ba. Idan ba a ci sa’a ba husuma ce za ta tashi. Sai dai kuma ba zancen ƙaranta a tsakaninsu domin kowa yana ƙoƙarin kare mutuncinsa kada a ga wallensa.

Sannan kuma babbar matsalar da za a fara fuskanta shi ne, mace za ta dinga ganin ba dole ta ga girman mijinta ba saboda tana ganin duk abinda yake taƙama da shi, ita ma tana da shi. Idan miji ma ya hore ta da hana ta wani abu, iyayenta za su yi mata. Sannan ba ta shayin yin duk abinda ta ga dama. Ba dai qarshe ka sake ta ba? Ta san tana fitowa za a yi ta rububinta ko ba don Allah ba. Don haka, idan ba mai tsoro Allah aka samu da gaske ba, ba lallai ta bi mijinta na aure ba. 

Idan Talaka ya auri ‘yaruwarsa Talaka akwai fahimtar juna da daidaito. Ba yadda za a yi wani ya ɗaga wa wani kai domin duk asalin ɗaya ne. Kuma ba mai yi wa wani gori. Matar ta saba da akwai da babu na yau da gobe kamar dai yadda samunsa yake.Sai dai fa akwai kallon raini da kar ta san kar. Babbar matsalar da za a fara samu ita  ce, yadda za su kasance a halin babu kuma ba mai iya tallafar wani. Shi miji ɓangarensa da danginsa babu, ita kuma ma matar haka. Duk matsalar kuɗin da ta taso fa shi mijin shi ne mai kula da ita. Wataƙila ma nauyin gidansu da na ƙannensa dukka suna wuyansa. Wani zubin ma dangin matar ko iyayenta suna hangen me za su samu ta wajensa. Sai ka ga mutum duk ya bi ya rikice lokaci guda. Zancen ƙaranta da ma gidan aka zo. Ba wani kara a cikin lamarin. 

Don haka a ganina maslaha kawai ku auri wacce ko wanda kuke ƙauna kuma za ku iya jure duk wani juyin rayuwa mai daɗi da maras daɗi har ƙarshen rayuwarku. Haka ku auri waɗanda suke da tarbiyya da ilimin addini. Da arziki da rashinsa duk na Allah ne. Kuma mai iya canza lamurransa ne duk lokacin da ya so. Sai dai mu ce Allah ya ba mu dacewa. 

A ƙarshe na ke godiya ga makaranta da suke jimirin karatun wannan fili a kowanne lokaci. Sannan su kira su yi fatan alkhairi da tsokaci da shawara. Kullum kuna raina kuma ku ne kuke ƙarfafa min gwiwa a kullum. Na gode. Mu haɗu a wani makon idan Allah ya kai rai.