Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban APC na ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC ta bayyana Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugabanta na ƙasa a ci gaba da gudanar da babban taronta.

Shugaban Kwamitin Zaɓe na babban taron na APC, Gwamna Abubakar Badaru, shi ne ya bayyana Sanata Abdullahi Adamu wanda ɗan asalin jihar Nasarawa ne a matsayin sabon shugaban jam’iyyar tasu ta APC bayan da duka sauran abokan takarar Adamu suka miƙa wuya suka yi masa mubaya’a.

Haka nan, Badaru ya lissafo wasu muƙamai waɗanda babu buƙatar kaɗa ƙuri’a inda ya yi amfani da zaɓen jin ra’ayi wajen tabbatar da muƙaman ga masu su.

Sai dai muƙamin Sakataren Jam’iyya na ƙasa na daga cikin manyan muƙaman da ake ci gaba da fatatawa a kai kasancewar ‘yan takarar sun kasa cimma sulhun sallama wa mutum guda daga cikinsu.

Shugaban kwamitin zaɓen ya ce daga cikin ‘yan takara huɗun da ke neman muƙamin sakataren jam’iyyar mutum guda ne kawai ya amince ya janye.

Sauran ‘yan takarar da suka rage a fagen neman muƙamin sakataren su ne: Prof. Olaiya Abideen Olaitan (Oyo), Otunba Iyiola Omisore (Osun) da kuma Barr. Adebayo Shittu (Oyo).

Gwamna Badaru ya buƙaci ‘yan takarar da su haɗu su fahimci juna sannan su fitar da mutum guda daga cikinsu da za a tabbatar da shi a muƙamin sakataren.