’Yan bindiga sun hana jirgin sama tashi a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu gungun ’yan bindiga sun hana wani jirgin saman AZMAN da ke shirin zuwa Legas tashi a ranar Asabar daga filin jirgin saman Kaduna.

Wata majiya ta tabbatar da cewa ’yan bindigar sun harbe wani ma’aikacin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Saman Nijeriya (NAMA), Shehu Na’Allah a kusa da titin jirgin da ke filin jirgin.

Majiyar ta bayyana cewa, jirgin na AZMAN bai iya tashi da misalin ƙarfe 12:30 na dare ba saboda kasancewar ’yan bindigar a titin filin jirgin.

“Kamar yadda na ke magana da ku a yanzu, akwai sojoji da dama da ke sintiri a wurin dob ƙarfafa tsaro, kodayake yawancin ma’aikatan na fargabar kada a kashe su, inji majiyar.

Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, manajan filin jirgin, Misis Amina Salami, ta ce ’yan bindigar sun mamaye filin jirgin ne ta shingen dajin da ke kusa da wajen da misalin ƙarfe 1:00 na yammacin ranar Asabar, inda suka fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa don tsorata ma’aikatan.

Majiyar ta ce, sama da manyan motocin sojoji 10 ne ke filin jirgin a halin yanzu domin ƙarfafa tsaro.