2023: Wasu ‘yan takarar shugabancin Nijeriya uku za su dunƙule wuri guda

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Jiga-jigan masu neman tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, Abubakar Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal da Bala Abdulkadir Mohammmed sun yanke shawarar haɗa kansu domin cimma buƙatar yi wa ƙasar nan jagoranci a shekara ta 2023.

Wannan shawara tasu ta biyo bayan wani zama ne da su uku suka gudanar a garin Bauchi a kwanakin baya, inda suka yi wata tattaunawar shirri ta fiye awowi biyu a cikin wani zaure dake gidan gwamnati, suna masu nazarin cewar. zaman lafiyar ƙasar nan, cigaban ta da bunƙasar ta sun shallake son zuciyar daidaikun su.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki wanda ya yi wa manema labarai jawabi a madadin su ya ce, “mun yi yaƙinin zama akan shawara tamu tayin aiki tare, mun gaskata cewar, cimma muradun ɗaiɗaikun mu bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta da buƙatun ƙasar mu ta Nijeriya.”

Suka ce, “akwai buƙatar a garemu na wanzuwar haɗin kai, mun yi yaƙinin dukkan mu uku za mu iya yin aiki tare cikin lumana, hazaƙa da kuma karsashi, ta yadda za’a samar wa da ƙasar nan wata manufa ta gari anan gaba.

“Mun kuma yarda da cewar, ko wannen mu ya nuna sha’awar yi wa ƙasar nan jagoranci, mun kuma yi la’akari da cewar, ko wannen mu ya kai munzali da karsashin iya jan ragamar ƙasar nan, amma kuma daga qarshe mutum ɗaya ne ƙwal zai kasance shugaba a shekara ta 2023.”

Sanata Abubakar Saraki ya bayyana cewar, su ukun sun yi matuƙar kaɗuwa da ganin yadda ‘yan Nijeriya suke cikin matsanancin rayuwa bisa ga tsadar rayuwa na yadda farashin ababen more rayuwa suka yi tashin gwauron zabi, suna masu nuni da cewar, jam’iyyar PDP ita ce kaɗai za ta kai jama’a bakin gaci, ta kuma ceto da al’ummar ƙasar nan daga ƙangin matsaloli da suka dabaibaye ta.

“Yan neman shiga takarar dai guda uku sun yi tababar cewa, a matsayin sun a masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP, akwai bukatar su haɗa kan su wuri guda, da zummar ganin yadda zasu samar wa ƙasar nan shugabanci nagari da mafita daga cikin ƙalubaloli na rayuwa.

“Mun kuma yanke shawarar yin aiki tare ƙud-da-ƙud domin mu samar da wata hanya ta dunƙule wa zuwa abu guda ta yadda zamu ciyar da ƙasar nan zuwa gaba. Mun kuma yi yaƙinin taka rawa na samar wa ƙasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali, domin idan akwai kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar PDP, za a samu lumana da kwanciyar hankali a ƙasar nan,” inji Saraki.

Ya shaida wa manema labarai cewar, za su kuma bayyana wa babban su, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ire-iren abubuwa da suka tattauna akai a zaman su na garin Bauchi, na cewar, za su yi aiki tare, haɗi da fifita Nijeriya fiye da burace-buracen ɗaiɗaikun su, kuma za su cigaba da yin irin wannan taro.

Saraki sai ya bayyana cewar, babu wani daga cikin su da zai yi magana da bakin wani da bai halarci taron nasu ba, “amma kuma mun yarda  mu yi mussayar ra’ayi a tsakanin mu da Wazirin Adamawa, kuma muna da ƙwarin gwiwar zai yi nasa tsokaci a kan abubuwan da muka tattauna a garin Bauchi.”

Ƙwararren ɗan siyasar dai na jihar Kwara saboda haka ya yi kira wa magoya bayan su da su guji yin musayar yawu a tsakanin su, la’akari da cewar, su kansu a dunƙule yake, babu wani kace-nace a tsakanin su, yana kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewar, da ikon Allah akwai hasken annuri a gaban su.

Jiga-jigan jam’iyyar na PDP guda uku, sun kuma yi yaƙinin cewar, APC ba jam’iyya ba ce, ganin yadda ta gagara shawo kan matsalolin da ‘ya’yan ta suke ciki na neman shugabancin ta, suna masu cewar, duk wanda ya kasa gudanar da mulkin jam’iyya, ba zai iya gudanar da mulkin ƙasar nan ba.

“Saboda haka, damar da kawai ta rage wa ‘yan Nijeriya ita ce ta rungumar jam’iyyar PDP, kuma muna da yaƙinin cewar, ta wannan hanya ce za mu shure muradun mu na ɗaiɗaiku, ya zuwa ga muradun ƙasa. Kuma muna ganin wannan zama da muka yi wani sharar hanyar Nijeriya ce ta zuwa tudun mun tsira.”