Rikicin Ukraine: Fesbuk ya haramta wa Rasha tallata kasuwanci a shafinsa

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin sadarwa na yanar gizo na Fesbuk wanda a yanzu ya rikiɗe ya koma Meta ya haramta wa ƙasar Rasha tallata kasuwanci a shafukansa.

Wato dai dukkan kafafen yaɗa labarai mallakin ƙasar, kamfanin ya hana su tallata komai a dandalin na sada zumunta (Fesbuk).

A yanzu haka ma dai Kamfanin na Fesbuk wanda aka fi sani da Meta ya dakatar shafukan wasu manyan kafofin yaɗa labarai mallakin ƙasar ta Rasha guda huɗu. 

Wannan jawabi na haramci ga ƙasar Rasha ya fito ne daga shafin Tiwita na shugaban sashen tsaro na kamfanin Meta (Fesbuk), Nathaniel Gleicher.

Inda ya ƙara da cewa, duk wani talla da hada-hadar da ta shafi kasuwancin kamfanin nasu ya dakatar da ƙasar Rasha daga yi a dandalinsu. 

Inda shugaban sashen tsaro na Meta ya rawaito a shafinsa na Tiwita cewar: “A halin yanzu mun haramta wa duk wata kafar yaɗa labarai mallakin ƙasar Rasha yin talla, ko wata harkar kuɗi a dandalinmu. Kuma za mu cigaba da sanya alama ga dukkan kafafen yaɗa labarai mallakin Rasha”. 

Sannan ya ƙara da cewa, za su cigaba da ɗaukar wannan mataki ne. Sannan kuma za su cigaba da lura da al’amuran da suke cigaba da afkuwa a ƙasar Ukraine, a lokaci guda kuma, su cigaba da faɗakar da mutane irin matakan da za su ɗauka kariyar asusunsu a dandalin (Fesbuk).

Ita wannan sanarwa ta haramcin ta biyo bayan wata sanarwa da ta fito daga bakin, Roskomnadzor wato majalisar zartarwa ta ƙasar Rasha wacce take da alhakin kula, tacewa, da ƙayyade harkokin kafafen yaɗa labarai a qasar. Inda a ranar Juma’ar da ta gabata aka bayyana cewa, majalisar ta ba da sanarwar cewa, za ta sanya dokar rage shiga Fesbuk sosai a ƙasar. 

Idan za a iya tunawa a baya, Jaridar Nairametrics ta rawaito cewa, mahukuntan Fesbuk sun sanya takunkumi a kan bayanan kutsen Rasha a ƙasar Ukraine. Inda ita kuma Majalisar Roskomnadzor ta aike da wasiƙa zuwa ga Kamfanin a kan a cire wancan takunkumi domin a cewarta, hakan rashin adalci ne da cin zarafin ‘yancin yaɗa labarai. 

Kamfanonin yaɗa labaran mallakin rasha da Fesbuk ta sanya wa takunkumi sun haɗa da: Gidan talabijin na , Zvezda TV;  Kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti, da  kuma zaurukan yanar gizo na Lenta.ru da kuma Gazeta.Ru.  A cewar Roskomnadzor, sun nemi Fesbuk su saurare su, sannan su cire musu takunkumin amma sun yi buris da su.  

Shi ma Nick Clegg wani ƙusa ne a kamfanin na  Meta ya rawaito a shafinsa na Tiwita cewa, ƙasar Rasha ta nemi Fesbuk su daina tace labarurrukan da sassan yaɗa labaranta suka watsa a dandalin Fesbuk, su kuma suka ƙeƙasa ƙasa.