Ana cigaba da yi wa Abba Kyari tara-tara

*Ministan Shari’a da Hukumar NDLEA sun garzaya kotu rana ɗaya
*Me zai faru idan kotu ta amince da buƙatun ɓangarorin biyu?

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Daga dukkan alamu tsugunne ba ta ƙare wa fitaccen ɗan sandan Nijeriya nan, DCP Abba Kyari ba, inda a cikin makon nan mai ƙarewa gwamnatocin Nijeriya da Amurka ke cigaba da yi masa tara-tara a gaban kuyliya, don hukunta shi sakamakon zarge-zargen da suke yi masa masu alaqa da damfara da kuma laifin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, lamarin da ya sanya Hukumar FBI ta Amurka ke neman Kyari ruwa a jallo har ma ta nemi Gwamnatin Nijeriya ta tuso mata ƙeyarsa, don fuskantar tuhumar aikata damfara da haɗin baki. Ana cikin haka ne kuma, sai Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya ta damƙe ɗan sandan bisa zargin haɗin baki wajen ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

A jiya ne dai Ma’aikatar Shari’a da Hukumar NDLEA suka shigar da ƙara kan bautuwan.

Yadda Gwamnatin Nijeriya ta amince ta miƙa wa Amurka Kyari:
Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya bayar da wata sanarwa a cikin makon nan, yana mai bayar da bayani kan batun miƙa DCP Kyari ga Amurka, wanda tuni Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta dakatar da shi.

Bayanan sun nuna cewa, Gwamnatin Nijeriya ta amince da miƙa DCP Kyari ga Amurka bisa zargin aikata damfara, almundahanar kuɗi da hada-hadar sata da kuma alaƙa da wani gawurtaccen ɗan damfara, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, wanda ya amsa laifin aikata laifin damfarar intanet. A watan Afrilu na 2021 ne wani kwamitin alqalai ya yanke wa Kyari hukuncin kama shi da laifi bisa amincewar Kotun Yanki ta Gundumar Tsakiyar Kalifoniya da ke Amurka. Don haka Amurka ta nemi Nijeriya ta miƙa mata shi a matsayinsa na ɗan Nijeriya, don fuskantar hukuncin da ya dace da shi.

A ranar Larabar nan, 2 ga Maris, 2022, Ministan Shari’a Malami (SAN) ya shigar da buƙata a gaban Alƙalin Alƙalan Babbar Kotun Tarayya a Abuja yana neman a ba shi izinin miƙa DCP Kyari ga Amurka.

A cikin sanarwar da Kakakin Ministan, Umar Gwandu, ya sanya wa hannu a jiya Alhamis, ya yi bayani kan laifukan da suka shafi fita da shi Kyarin zuwa ƙasar waje.

Ya ce, “kamar yadda ku ka sani, batun miƙa wani ga wata ƙasa abu ne wanda ya shafi ɓangarori daban-daban. Abubuwa ne da yawanci suka haɗa ƙasashe ba guda ɗaya ba, ƙasa da ƙasa, cikin gida da kuma sashen shari’a.

“Wata ƙasa ta nemi a miqa mata ɗan wata ƙasar ga hukumomi, ɗaya ne daga cikin waɗancan abubuwa da lamarin ya shafa. Ofishin Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a ya amshi buƙatar miƙa jami’in da ake batu a kan sa.

“Bayan dogon nazari kan lamarin bakiɗaya, Ofishin Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a ya shirya batun kuma ya miƙa shi ga hukumomin da lamarin ya shafa, don ɗaukar matakan da suka dace.

Laifukan da Hukumar NDLEA ke tuhumar Kyari da su a gaban kotu:
Hukumar Yaƙi da Ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ya gurfanar da DCP Abba Kyari tare da wasu yaransa guda huɗu a gaban kotu bisa tuhumar sa da aikata manyan laifuka guda takwas da kuma guda shida masu alaƙa da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Sauran mutane huɗun da ake tuhumar sa tare da su sune, jami’an da suka yi aiki a ƙarƙashin tawagarsa ta tsaro ta musamman, waɗanda suka haɗa da ACP Sunday J. Ubia, ASP Bawa James, Insp. Simon Agirigba da Insp. John Nuhu, sai kuma wasu waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da aka cafke a Filin Jiragen Sama na Akanu Ibiam International Airport da ke Enugu, wato Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

A jiya ne Hukumar NDLEA ta miƙa fayil ɗin tuhumar mai lamba FHC/ABJ/57/2022, ta hannun lauyanta kuma Daraktan Sashen Shari’a na Hukumar, Mista Joseph Sunday, inda ta ke tuhumar su da aikata laifuka kamar na haɗin baki, kawo naƙasu, harkar hodar ibilis mai nauyin kilogiram 17.55 da sauransu.

Hukumar NDLEA ta shigar da tuhume-tuhumen ne awanni kaɗan bayan da Minista Malami ya miqa buƙata da Babbar Kotun Tarayya, don amincewarta wajen bai wa Gwamnatin Nijeriya izinin miƙa Abba Kyari ga Ƙasar Amurka, don amsa tuhuma, wacce ta haɗa har da damfarar zunzurutun kuɗi Dalar Amurka Miliyan 1.1.

Yanzu dai abinda ya rage a gani shine, yadda za ta kasance kan waɗannan shari’u guda biyu da ke kan fitaccen ɗan sanda da kuma yadda za a iya warware su ba tare da kowanne ɓangare na ƙasashen ya yi asarar komai ba ko kuma ya kasa samun abinda ya ke muradi.

Akwai dai yarjejeniya tsakanin Nijeriya da Amurka kan batun shari’a da tuhume-tuhume, wacce a yanzu hakan ne ya bai wa ƙasashen biyu damar musayar waɗanda ake tuhuma a tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *