‘Yan kasuwa sun fusata da sabuwar dokar CBN kan sufuri

Daga AMINA YUSUF ALI

’Yan kasuwa masu shigo da kaya daga ƙasashen waje zuwa Nijeriya sun caccaki sabuwar dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN) a kan harkar fatauci. Sannan kuma sun gargaɗi al’umma a kan hauhawar farashi da tsadar rayuwar ma gabaɗaya. 

‘Yan kasuwar sun nuna tsananin ɓacin ransu game da dokar da CBN ta kafa a kan tilas kowanne ɗan kasuwa mai shigo da kayan ƙasar waje ya yi rajista a zauren yanar gizo na CBN ɗin, sannan kuma tilas ya amince da tsarin daidaita farashi da Bankin ya tsara. 

A kan haka ‘yan kasuwar suke gargaɗin al’umma da su sa rai da hauhwawar farashi da ƙarin matsin rayuwa.

A cikin watan Janairun shekarar nan ne, 2022 dai ne CBN ya sanar da sabuwar dokar wacce ta tilasta wa dukkan fataken da su yi rajistar yanar gizo da bankin, sannan kuma su bi dukkan sabbin dokoki da tsare-tsaren da ya tanada wanda ya haɗa har da biyan dalar Amurka 350 a matsayin kuɗin sabunta rajistarsu ta kowacce shekara.