Koyi da Saudiyya: Za a fara fille kan masu ta’ammalli da miyagun ƙwayoyi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙudirin dokar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, wanda ya ƙunshi kisa, ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar Dokoki ta Jihar Kano.

Majalisar Dokokin Jihar Kano dai ta ce za ta duba yiwuwar yin wata doka kwatankwacin irin ta Ƙasar Saudiyya da za a riƙa fille kan duk wanda aka same shi da ta’amalli da miyagun ƙwayoyi ko kuma safararsu. 

Kakakin Majalisar Dokokin ta Jihar Kano, Rt. Hon. Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tsokaci kan yadda matasa da ‘ya’yan masu faɗa-a-ji suke yawan ta’amilli da miyagun ƙwayoyi.

Majalisar ta ce babu abinda ya dace a ɓullo da shi a matsayin hanyar hukunci shi ne kamar da waccan doka wacce za ta nuna ba sani ba sabo kan wanda aka samu suna ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi ko kuma suna sha. 

Shugaban majalisar ya ce “za mu bai wa wannan dokoki kulawa, kuma za mu tabbatar da an yi tanade-tanade na hukunci mai zafi musamman ga masu shigo da ƙwaya a wannan jiha ta mu ta Kano.

“Wasu ƙasashen irin hukuncin da suke ɗauka ga masu shigar da ƙwaya kisa ne kawai kamar su Saudiyya to muma In sha Allah za mu duba za mu tabbatar da cewa an ɗauki matakai masu tsauri,” inji Chidari.

Shi ma a tasa gudunmawar Hon. Iliyasu Ali Danja ya ce sun lura da cewa ‘ya’yan shafaffu da mai ne suka fi yin ta’ammuli da miyagun ƙwayoyin kuma su ne suke lalata rayuwar ‘ya’yan ya-ku-bayi, don haka ya ce ya zama wajibi majalisar ta ɗauki matakin ba sani ba sabo, domin daƙile wannan al’amari.