Ma’aikata ta nesanta kanta daga sanarwar bogi

Daga BASHIR ISAH

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ta nesanta kanta daga wata sanar da ke nuni da ‘yan ƙasa su dakatar da tafiye-tafiye zuwa wasu keɓaɓɓun ƙasashen waje har zuwa ƙarshen watan Mayun 2022.

Cikin sanarwar manema labarai da Ma’aikatar ta fitar a jiya Talata, ta ce sanarwar dakatar da tafiye-tafiyen ba gaskiya ba ne kuma ba daga gare ta take ba.

An ga wata sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 18/02/2022 da aka yaɗa mai nuni da hana ‘yan Nijeriya tafiye-tafiye zuwa ƙasashen da suka haɗa da; Belarus, Poland, Slovakia, Hungary, Romania da kuma Moldova wai har sai zuwa ƙarshen watan Mayu, saboda wai ofishin jakadancin waɗannan ƙasashen sun daina bada bisa ga matafiya.

Tare da cewa, ‘yan Nijeriya su guji kasadar ziyartar ƙasashen da ke maƙwabtaka da ƙasashen Rasha da Ukraine saboda zargin da ake yi na cewa yaƙi na iya ɓallewa a tsakanin ƙasashen a kowane lokaci.

Yin arba da wannan sanarwar ya sanya Ma’aikatar hanzarta fitowa ta ƙaryata da kuma nesanta kanta daga gare ta tare da bayyana sanarwar a matsayin ta bogi.

Ma’aikatar ta ce sanarwar bogin mai ɗauke da kwanan wata 18 ga Fabrairu, 2022, shirin masharranta ne kawai, hasali ma sa hannun da ke kan sanarwar da takardar da ma tsarinta duk ba na ma’aikatar ba ne.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Mrs Francisca K. Omayuli ta ce Ma’aikatar ta ƙaryata wannan labari ta kuma yi tir da shi. Daga nan, Ma’aikatar ta buƙaci al’ummar ƙasa da su yi fatali da sanarwar bogin.

Ta ƙara da cewa, duk sanarwar da take fitarwa takan yi amfani da hanyoyin da ta saba amfani da su ne a hukumance wajen isar da saƙonninta ga jama’a.