Ɗangote ya zarce mamallakin Chelsea a arziki

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai, mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Ɗangote, ya sake shillawa sama a cikin jerin sunayen mutanen da suka fi kowa arziki a Duniya. Domin kuwa rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu haka ma sunan Ɗangote yana saman sunan Biloniyan attajirin nan na ƙasar Rasha, Roman Abramovich. Kuma mamallakin kamfanin ƙwallon ƙafa na Chelsea.

Jaridar Bloomberg ta rawaito cewa, a  yanzu haka ƙarfin arzikin attajirin kuma biloniya, Aliko Dangote ya ƙara haɓaka da ƙarin, Dalar Amurka $934 abinda ya kai shi ga zama mutum na 83 ma fi arziki a Duniya. Sannan kuma jimillar ƙarfin arzikinsa ya kama, Dalar Amurka biliyan 20.  Wannan shi ne dalilin da ya sa ya doke attajirin nan mamallakin kamfanin ƙwallo na Chelsea a arziki. 

Bugu da ƙari, a yanzu haka ma, ya kere kamfanonin Airtel da MTN a ƙarfin arziki. 

Rahotanni sun bayyana cewa, ƙarfin samun arzikin Ɗangoten na da alaƙa da yadda kamfanoninsa na sumunti suke ƙara haɓaka. Don haka, idan aka samu faɗuwa ma, sai a ga ƙarfin arzikin nasa ma ya ragu. 

Idan ba za a manta ba, a watan Janairun nan da ya gabata, Ɗangote shi ne mutum na 97 daga jerin sunayen mutane 500 da suka fi kowa arziki a Duniya. A wancan lokacin ƙarfin arzikin attajirin shi ne, biliyan $19.2. Amma a halin yanzu da ake rubuta wannan rahoton, Ɗangote yana matsayin mutum na 83 a jerin mafiya kuɗi na Duniya. Wato kamar yadda aka faɗa, ya zarce attajirin nan ɗan ƙasar Rasha mamallakin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea a arziki. Shi  kuma Roman Abramovich ɗin ya faɗo i zuwa na 124 a jerin.

A wata hirarsa da jaridar Ingilishi ta Bloomberg, Ɗangote ya nanata irin burin da yake da shi na saye ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal. Amma a cewarsa, sai ya kammala aikin da yake gabansa na ganin ya ƙarasa aikin ginin matatarar man da yake so ya buɗe a Nijeriya, nan ba da daɗewa ba a cikin shekarar 2022 da muke ciki.

Matatar ana sa ran za ta kawo ƙarshen wahalar man fetur da ake fama da ita a Nijeriya. Sannan ta samar wa da Nijeriya kuɗin shiga da ya kai Dalar Amurka biliyan 11 a kowacce shekara.