Yajin aikin ASUU: Zaman sasantawa ya tunzura ministan ilimi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Ministan Ilimi na Ƙasa, Mallam Adamu Adamu a ranar Litinin ce da ta gabata ya nuna tuzurin fushi, tare da fita daga ɗakin taron sasantawa tare da wakilan ɗaliban ƙasar nan (NANS) waɗanda suke yin bore bisa yawan shiga yajin aiki da ƙungiyar jami’o’in ƙasar nan (ASUU) suke yi.

Ministan dai, ya shirya wani taro ne na ba-za-ta da shugabannin ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS), waɗanda suka yi cincirindo a mashigar ma’aikatar Ilimi ta tarayya (FME) da ke Abuja a ranar Linitin da ta gabata.

Ɗaliban na ƙasa, sun nemi ministan ne da ya rufe ofishin sa, la’akari da cewar, ya gaza samun hanyoyin daidaito wa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i na Ƙasa (ASUU), yayin da gwamnatin ta kasa taɓuka komai dangane da yawan yajin aiki da malaman jami’o’i suke yi babu ƙaƙƙautawa shekara da shekaru.

Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban na ƙasa, Kwamared Sunday Asefon, ya ce, “yajin aikin ASUU yana yi wa fannin ilimin ƙasar nan kisan mummuqe. Yaje-yajin aiki na malaman yana ƙuntata wa rayuwar mu tun daga shekarar 1999, don haka ɗalibai suke buƙatar kasancewa a cikin tattaunawa da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malamai ta ASUU da zummar samo bakin zaren.

“Muna buƙatar Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar ASUU su gaggauta janye yajin aiki da malamai suke ciki a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da tattaunawa a tsakani. Muna son komawa ajujuwa domin ci gaba da karatu, idan kuma ba haka ba, wannan bore namu zai gwammace gwamma tashin-tashinar ‘#EndSARS.’

Rashin jituwar a yayin zaman tattaunawar ya fara ne lokacin da shugabancin ɗaliban yake zargin minista da dagula lamuran ilimi na ƙasar nan, yayin da yake tura ‘ya’yan sa suna yin karatu a ƙasashen ketare.

Minista Adamu, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa da kalaman da ɗaliban suke yi, ya ce sun ba shi kunya bisa waɗannan kalamai nasu, kwatsam kuma sai ya tashi tsaye da fushi, ya fice daga ɗakin tattaunawar dake cikin hurumin ma’aikatar ta ilmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *