Yadda gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ke cigaba da kankama a majalisa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dattawan Nijeriya ta kaɗa ƙuri’a kan wasu sassa sittin da takwas na kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 da suka ƙi amincewa da ƙirƙirar wa mata kujera na musamman.

“Ƙudirin ya nemi a samar da muƙamai na musamman ga mata a Majalisar Dattawa, Wakilai da Majalisar Jiha ta hanyar samar da kujeru guda na musamman a kowace jiha ta tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya da aka keɓe wa mata kaɗai ba tare da la’akari da cancantarsu ta tsayawa takara ta kujerun sanatoci a kowace jiha da Abuja ba.

“Ga Majalisar Wakilai, ƙarin kujera biyu ne ga kowace jiha da kuma babban birnin tarayya Abuja da za a keɓe wa mata ba tare da la’akari da cancantar tsayawa takarar sauran kujerun ba. Kuma a ƙarshe ga Majalisun Dokokin kowace Jiha an ware ƙarin kujera ɗaya daga kowace mazacar Sanata uku ga mata. Wannan shi ne don ƙarfafa mata shiga da wakilci a cikin shugabanci.”

Sai dai daga cikin Sanatoci 91 da suka yi rijistar kaɗa ƙuri’a a kan wannan batu, 30 sun kaɗa ƙuri’a na’am, 58 kuma suka qi amincewa, 3 kuma suka ƙi amincewa, lamarin da ya zube ƙasa warwas kenan. Wani sashe kan samar da kujera (Sashe na 68), wanda ke neman sauya kundin tsarin mulkin ƙasar don samar da mafi ƙarancin kaso goma na mata da aka zaɓa a matsayin ministoci da kwamishinoni a majalisar zartarwa ta tarayya da na Jihohi, domin hakan zai tabbatar da shigar mata cikin harkokin mulki ya kasa cika sharuɗɗan.

Matakin dai ya buƙaci goyon bayan aƙalla Sanatoci 73, amma ƙuri’ar amincewa da ƙuri’u 44 ne, yayin da 43 suka ƙi amincewa. Samar da kujeru ga mata a cikin harkokin mulkin jam’iyyar siyasa, wanda ke buƙatar ƙananan kashi 35 na mambobin zartarwar jam’iyya a dukkan matakai su ma sun gaza. An kayar da shi da ƙuri’u 53 “a’a” 34 “e” da 3 suka ƙaurace.

Sai dai a yayin kaɗa ƙuri’a, daga cikin Sanatoci 95 da suka yi rajistar kaɗa ƙuri’a a kan ƙudirin 41 sun kaɗa ƙuri’a a yayin da 44 suka ƙi amincewa da shi. Wannan babbar nasara ce ga jihohi irin su Legas da Ribas da suka samar da nasu ma’aikatar kuɗaɗen shiga (IRS) har ma sun kai ƙarar gwamnatin tarayya kan hakan.

Ƙudirin samar da rawar gani ga Sarakunan Gargajiya da cibiyoyi ma ya ci tura. Mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulki na majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya yi namijin ƙoƙari wajen ganin an ceto magana ta 18 a kan gyaran shari’a, amma Lawan ya tsaya tsayin daka cewa a mutunta abin da suka yi, domin hakan na iya buɗe wasu sabbin buƙatu na wasu sharuɗɗan. Sanata Kabiru Gaya, Kano ta Kudu ya goyi bayan Omo-Agege ya kuma ƙara da cewa, a sake duba batun sarakunan gargajiya.

Abdullahi Adamu ya yabawa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kan yadda ya jagoranci zaman majalisar na ranar, sai dai ya ce za a iya sake duba batutuwa masu muhimmanci kamar su muƙamai na sarakunan gargajiya tunda ‘yan majalisa mutane ne masu iya yin kuskure.

Sai dai Ali Ndume ya ce, ba za su iya zama su juya wa kansu baya ba, yana mai cewa za a iya gyara kundin tsarin mulkin ƙasar nan da wasu shekaru masu zuwa. Lawan da ke goyon bayan wannan matsayi ya ce, idan wasu ba za su iya samun abin da suka yi zagon ƙasa ba, to su haƙura da majalisar dattawa.

Bayar da ikon cin gashin kai ga ƙananan hukumomi, haɗa da jami’an tsaron Nijeriya da jami’an tsaro na farin kaya, da samar da abinci na daga cikin muhimman sharuɗɗan da majalisar ta bayar a ranar Talata.