Dokar hana ci da safarar jakai babbar illa ce gare mu, cewar dilolin jakai

Daga AMINA YUSUF ALI

Diloli masu safarar jakuna a faɗin Nijeriya sun koka matuƙa a kan dokar da gwamnatin tarayya ta riga ta zartar a kan hana ci da safarar jakunan. 

Shugaban ƙugiyar dilolin jakuna ta Nijeriya, Mista Dike Ifeanyi shi ya bayyana haka a yayin zantawar sa da manema labarai a game da dokar hana safara da cin jakunan da sayar da abinda ya shafe su da gwamnatin Nijeriya ta sanya a ‘yan kwanankin nan. Inda ya bayyana wasu daga cikin alfanun kiwatawa da cinikin jakunan a ƙasar nan. 

Daga cikin falalar jakunan a cewar sa, sun haɗa da, samar da aikin yi ga fiye da mutane dubu hamsin a ƙasar waɗanda suke cin abinci a ƙarƙashin harkar. Kuma dukkansu matasa ne. Tun daga maƙera wuƙar da ake aikin, har ya zuwa masu sarrafa fatar zuwa barguna da sauransu. Banda kuma sinadarai masu amfani da suke ƙunshe a cikin naman jaki. 

Sannan kuma a cewar sa, ga samun kuɗin shiga ga gwamnatin Tarayya. Domin lokaci ya yi da gwamnati za ta yi koyi da ƙasashe kamar Kenya da Pakistan wajen rage dogaro da man fetir.

Don haka Mista Ifeanyi ya ce, dokar hana fataucin jakunan za ta jawo dukka waɗancan matasa su rasa ayyukan yin nasu. Kuma a cewar sa dole sai sun samu aikin da za su tallafi kansu. 

A cewarsa, hakan zai iya taimaka wa wajen cigaba da tavarvara harkar tsaro a ƙasar nan. Domin rashin samun tudun dafawa na iya  jefa su a cikin ƙangin talauci da zai iya sa su iya shiga harkar ta’addanci. Domin da ma wuraren da suke yin aikin fiɗar jakunan cikin dazuzzuka ne. 

Kuma a cewar sa, lokaci ya yi da za Gwamnati za ta rage dogaro da man fetir ta koma kan wasu hanyoyin samar da arzikin.  Domin a cewar sa, mutane da yawa suna amfana da sana’ar wajen ɗaukar nauyin iyalansu da biyan sauran buƙatun rayuwa.