Ɗan jarida, Dahiru Muhammad ya zama Kachallan Kutumbawa

Daga WKAILINMU

Dakacin Kutumbawa a jihar Kano, Alhaji Mustapha Abubakar Rimin Kira ya amince da a naɗa ɗan jarida Dahiru Muhammad Maihula a matsayin Kachallan Kutumbawa.

Cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Dakacin Kutumbawa ya ce kwamitin naɗin ya amince da naɗin Dahiru Maihula ne duba da cewa shi hazaƙin mutum ne.

Yanzu haka Dahiru Maihula Darakta ne a wani kamfanin yaɗa labarai da ke Kano, wato DMM.

Sarakunan da Kano ta yi daga zuri’ar Kutumbawa sun haɗa da:
(1) Muhammadu Alwali Kutumbi.1623-1643
(2) Alhaji Dan Kutumbi.1648-1649
(3) Shekarau (ll) 1649-1651
(4) Muhammadu Kukuna.1651-1652
(5) Sarki Soyaki.yayi sarki sau biyu,1652
(6) Sarki Bawa. 1660-1670
(7) Sarki Dadi. 1670-1703
(8) Muhammad Sharif. 1703-1731
(9) Sarki Kumbari. 1731-1743
(10) Al-Hajj Kabe.1743-1753
(11) Sarki Yaji (ll) 1753-1768
(12) Baba Zaki.1768-1776
(13) Dauda Abasama (ll)1776-1781
(14) Muhammad Alwali.1781-1805

Masana tarihi na ra’ayin cewa wanda ya yi sarkin Kano, kafin jihadin Sheikh Usman Bin Fodio, wato Aliyu Yaji, ɗan zuri’ar Kutumbawa ne wanda ya yi aiki tuƙuru wajen yaɗa addinin Musulunci a Kano.

Haka nan, Sarki Aliyu Yaji ya yaƙi al’adar nan ta mutan Kano a wancan lokaci, wato “Dirki”

‘Dirki’ katafaren wuri ne kusa da Babban Masallacin Kano inda jama’ar Kano a wancan lokaci kan kai fatu su jibgi bayan yanka dabbobi yayin Babbar Sallah.

A wancan lokaci jama’a sun mayar da ‘Dirki’ wajen bauta na musamman inda suka yi amannar cewa wuri ne na karɓar addu’o’insu.