Ƙungiya ta nuna qin amincewa da ƙudirin majalisa na gabatar da kadarorin iyalan ma’aikatan banki

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani sabon ƙuduri da ‘yan majalisa suka shigar a  kan ma’aikatan banki a Nijeriya na sanya dokar dukkan ma’aikatan Banki su bayyana kadarorinsu da na mata ko mijinsu da kuma na ‘ya’yansu.

Ƙungiyar akawu (Ma’aikatan banki) ta Nijeriya ita kuma a nata ɓangaren, ta bayyana tsananin ƙin jininta a kan wannan sabuwar doka da ake son tabbatarwa a Nijeriya. Wacce ta tilasta wa duk wani ma’aikacin/ma’aikaciyar banki su gabatar da dukkan kadarorin da iyalansu suka mallaka. 

Kuma a halin da ake ciki har hukumar nan ta yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati, EFCC ta riga ta amshi wannan doka hannu bi-biyu tare da yin na’am da ita. 

Ƙudurin wanda ɗan majalisar Jihar Delta daga PDP, Francis Waive shi ya shigar da shi. Inda ya nemi a sanya hukuncin shekaru 20 a gidan yari ga dukkan mutumin da ya ƙetare wannan doka. 

Amma ita kuma a nata ɓangaren, Rita Adeyanju, lauyar ƙungiyar ma’aikatan banki ta bayyana a wata takardar tunatarwa da ta aike wa da kwamitin majalisar na hukumar EFCC ranar Alhamis ta bayyana cewa, wannan ƙuduri da ake son tabbatar da shi a doka, tamkar yin kutse ne ga sirrin iyalai da ‘ya’yan ma’aikatan banki. 

Sashe na 1(1) na dokar ya bayyana cewa,“Daga ranar da ma’aikacin banki ya fara aiki, ya aikata hakan. Shi kuma tsohon ma’aikaci an ba shi rarar kwanaki 30 ya bayyana rasitan dukkan kadarorin da ya mallaka da wanda mata/mijinsu suka mallaka da kuma na yaransu marasa aure da ba su haura shekaru 18 ba, i zuwa ga hukumar da take da alhakin lura da aikin.”

A cikin takardar da lauyar ƙungiyar ta aike zauren majalisa, ta bayyana cewa, wannan doka idan aka tabbatar da ita za ta ci karo da dokar kundin tsarin mulkin Nijeriya ta 37 ta shekarar 1999. Don haka, ta nemi a tsayar da dokar binciken kadarori a kan iya ma’aikatan banki, banda iyalansu. 

Haka ƙungiyar ta yi martani a game da dokar sashe na biyar wacce ta haramta wa ma’aikatan banki mallakar asusun ajiyar banki a wasu ƙasashen wajen Nijeriya. Domin a cewar su wannan doka ta yi tsauri matuƙa ga ma’aikatan bankuna.

Inda ƙungiyar take ba da shawarar sakar wa ma’aikatan mara su yi fitsari ta hanyar ba su damar mallakar asusun bankuna a ƙasashen waje.  

Sai dai kuma Hadiza Zubairu, shugabar ma’aikatan EFCC ta bayyana cewa, hukumar EFCC tana goyon baya ɗari bisa ɗari a kan wancan ƙudurin. Inda ta ce ana saran ma hukumar ta EFCC ita za ta jagoranci duba kadarorin iyalan ma’aikatan bankin. 

Hadiza Zubairu ta ƙara da cewa, wannan bincike yana da matuƙar muhimmanci domin irin kesa-kesan da ake samu na almundahanar kuɗi a bankunan Nijeriya. Kuma a cewar ta, abinda ya ci doma ba ya barin Awai. Domin su ma iyalan ma’aikatan bankin dole suna tare a cikin harƙallar. 

Idan ba za a manta ba, a shekarar bara ta  2021 ne shugaban EFCC Abdurrashid Bawa ya yamutsa hazo bayan ya bayyana cewa ma’aikatan bankuna za su fara gabatar da kadarorinsu daga ranar 1 ga Yunin shekara ta 2021.