Gwamnatin Kano za ta sake fasalin hukumomin Zakka da Hubsi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da sake fasalin hukumar Zakka da Hubsi ta jihar Kano, inda ta bayyana Dr. Ibrahim Mu’azzam Mai-Bushira a matsayin Shugaban Zartarwa.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talatar makon jiya, a ƙarshen taron majalisar da aka gudanar a ɗakin taro na Africa House dake fadar gwamnatin Kano.

A cewar sanarwar mambobin sun haɗa da Dr. Abdulmutallab Ahmed a matsayin kwamishina na ɗaya, Dr. Lawi Sheikh Atiq kwamishina na biyu na hukumar.

Garba ya kuma lissafa sunayen mambobin hukumar da suka haɗa da Sheikh Abdulwahab Abdallah, Alhaji Aminu Ɗantata, Alhaji Aliko Ɗangote da kuma Alhaji Abdulsamad Rabi’u, inji sanarwar.

Sauran mambobin, in ji shi, sun haɗa da wakilan masarautu guda biyar a jihar, wakilan ma’aikatar yaɗa labarai, ma’aikatar harkokin addini, wakilan kasuwannin Kurmi, Rimi, Kwari da kuma Singa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa “majalisar ta amince da kafa kwamitin tantance ƙungiyoyin addinin Musulunci na ƙasashen ƙetare, wanda Farfesa Sani Zaharaddeen, babban limamin Kano zai kasance a matsayin shugaba; Dr. Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini, mataimakin shugaba da Auwalu Shehu Yakasai a matsayin sakatare.’’

Sannan ya ƙarƙare da cewa “ofishin sakataren gwamnatin jiha ne zai samar da wakilan majalisar masarautu da hukumomin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *