Sin na goyon bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta kafar bidiyo, da shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a jiya Talata, inda ya shaida musu cewa, Sin tana matuƙar damuwa game da ɓarkewar yaƙi a Turai, tana kuma goyon bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ta yadda za a kai ga haye wahalhalu, da cimma sakamako mai amfani. Kazalika shugaban na Sin ya ce yana goyon bayan ƙasashen Faransa da Jamus, a fannin samar da daidaito, da tsari mai inganci na wanzar da tsaron Turai, bisa moriyar nahiyar.

Wannan ganawar ƙari ce kan wadda ta gabata, tun bayan da Faransa ta karɓi jagorancin karɓa karɓa na ƙungiyar tarayyar Turai ta EU, da kuma kama aikin sabon shugaban gwamnatin Jamus Mr. Olaf Scholz.

Sassan 3 sun maida hankali ga tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yanayi da ake ciki a Ukraine, inda kalaman shugaba Xi suka sake shaida cewa, har kullum Sin na goyon bayan adalci, game da rikicin dake faruwa, tana kuma bin matakai bisa tsari, da sanin ya kamata, da kare martabar ta a matsayin ta na babbar ƙasa.

Fassarawa: Saminu