Gaggauta goge bayanan ɗakin gwaje-gwaje ko me Amurka ke tsoro?

Daga CMG HAUSA

Ma’aikatar tsaron Rasha, ta ce a baya bayan nan ta gano bayanai game da wani shirin binciken ƙwayoyin halittu na ayyukan soji, wanda ƙasar Amurka ke samar da kuɗaɗen gudanarwa a ƙasar Ukraine, yayin da dakarun Rashan ke kutsawa Ukraine ɗin.

To sai dai kuma ya zuwa ƙarshen wata Fabarairun da ya gabata, ofishin jakadancin Amurka a Ukraine, ya gaggauta goge dukkanin bayanai masu nasaba da ɗakin binciken na Amurka daga kan shafin sa na yanar gizo. Ko shakka babu wannan rufa rufa ta sanya tambayar ko me Amurka ke tsoro?

Cikin ɗaruruwan ɗakunan gwaje gwajen kwayoyin halittu da Amurka ke da su a ƙasashen duniya daban daban ciki har da Ukraine, shin ko me Amurka ke boyewa?

Fassarawa: Saminu