Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki

Spread the love

Daga IBRAHIM YAYA

Ƙasa ta kan amsa sunanta ne a duniya, ko dai saboda ci gaban da ta samu a fannin tattalin arziki, ko kasuwanci, ko bincike a fannin sararin samaniya ko, fasahar ƙere-ƙere da sauran fannoni. Amma duk da irin wannan ci gaba da ƙasa ta samu, idan har babu zaman lafiya, tamkar ci gaba ne irin na mai hakar rijiya.

Ƙasashe irinsu Amurka dake ɗaukar kanta a matsayin ‘yar sandar duniya, ta kan bugi ƙirji a wasu lokuta ta riƙa ayyana kanta a matsayin ƙasar da babu kamar ta a dukkan fannoni a duniya. Sai dai ga mai bibiyar kafofin watsa labarai, ya san irin manyan ƙalubaloli da take fuskanta na yawan masu fama da annobar COVID-19 da waɗanda ke shekawa barzahu sanadiyyar cutar. Ga kuma uwa uba rashin kwanciyar hankali, sakamakon matsalar nuna wariyar launin fata da harɓe-harɓen bindiga da su ma ke haddasa hasarar rayukan jama’a da ba su san hawa ba balle sauka.

Sabanin ƙasar Amurka, wani rahoton aiki da kotun ƙolin jama’a ta ƙasar Sin (SPC) ta fitar, na nuna cewa, ƙasar Sin na daya daga cikin ƙasashen da suka fi zaman lafiya a duniya, baya ga kasancewarta ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya da kuma ci gaban da ta samu a fannin ƙirƙire-ƙirƙire na zamani, Rahoton wanda aka miƙa wa majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin domin tattaunawa, ya bayyana cewa, adadin manyan laifuffuka iri-iri guda takwas, kamar kisan kai, da fyade da kuma satar mutane, ya ragu matuka, yayin da yawan irin waɗannan laifuffuka shi ma ya ragu sosai.

Jagororin ƙasar Sin sun sha bayyana muradun ƙasar a wuraren taruka daban-daban, na ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ta hanyar mutunta juna da tattaunawa da daidaita sabani ta hanyar yin shawarwari maimakon yin fito-na-fito. Na baya-bayan nan shi ne, irin shawarwarin da ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi ya gabatar kan yadda za a daidaita duk wani rashin zaman lafiyar dake faruwa a sassan duniya, yayin taron manema labarai da aka kira a gyefen manyan tarukan ƙasar biyu dake gudana yanzu haka, wato taron majalisar wakilan ƙasar (NPC) da na majilisar ba da shawara kan harkokin siyasar ƙasar (CPPCC), ta yadda za a samu duniya mai zaman lafiya da wadata da kowa zai ji dadin zama a cikinta. Domin zama lafiya, aka ce ya fi zama dan sarki.

By Editor