Laifi tudu, Amurka ta taka nata ta hangi wasu

Daga AMINA XU

Kwanan baya, majalisar gudanarwa ta ƙasar Sin ta fitar da rahoto game da matsalar kare haƙƙin Bil Adama ta Amurka cikin shekarar 2021, inda aka gabatar da alƙaluma masu ɗimbin yawa dake bayyana yadda yanayin kare haƙƙin bil-Adama a Amurka ke ƙara tsananta. Duk da zanga-zangar da al’ummar Amurka ke yi game da wannan matsala, amma ‘yan siyasar ƙasar sun yi biris da wannan matsala, inda suka mai da hakali wajen tsoma baki cikin harkokin kare haƙƙin Bil Adama na sauran ƙasashe.

Lallai, ya kamata ‘yan siyasar Amurka su kalli kansu, su yi watsi da tunanin siyasantar da yanayin kare haƙƙin Bil Adama, su ɗauka matakan da suka dace a zahiri don kyautata haƙƙin dan-Adam na jama’ar ƙasar, maimakon kawo illa ga haƙƙin Bil Adama na sauran al’umma.

Mai zane: Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *