Birtaniya za ta ba wa Nijeriya Fam miliyan 10 don bunƙasa makamashi

Daga AMINA YUSUF ALI

Birtaniya ta yi alƙawarin bayar da Fam Miliyan ɗari ga sashen samar da makamashin Nijeriya.

Ministan ƙasar Birtaniya a kan harkokin Afirka, Vicky Ford, ita ta ba da wannan sanarwar a ranar Litinin ɗin da ta gabata. Inda ta bayyana cewa, ƙasar Birtaniyan za ta ba wa Nijeriya tallafin Fam Miliyan 10 don bunƙasa harkar makamashi. 

A cewar Malama Vicky Ford, ƙasar tasu za ta ba da tallafin ne ga Nijeriya domin bunƙasar sashen makamashi na ƙasar don samar da sauƙi a kan fanshon ma’aikatan sashen da sauran al’amuran tafiyar da harkar bunƙasa makamashi a Nijeriya.

A cewar ta, wannan tallafi zai sa ‘yan kasuwa su zuba jari kuma su mayar da hankali wajen samar da wuta da makamashi da ba lallai sai ta hanyar wutar lantarki da aka saba ba. Misali, za a iya amfani da hasken rana wajen samar da wutar da makamashi. 

Sannan ta ƙara da cewa, wannan al’amari ya nuna ƙarara irin kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna dake akwai a tsakanin Nijeriya da kuma ƙasar ta Birtaniya. Sannan kuma da irin kyakkyawan ƙudurin ƙasar don ganin ta tallafa wa Nijeriya musamman ta ɓangaren samar da makamashi. 

Shi ma a cewar sa, ƙaramin Minister makamashin Nijeriya, Godwin Jedy-Agba, ya bayyana cewa, Da ma ƙasar Nijeriya ta fara tunanin wata hanyar samar da wutar ba lallai sai ta lantarki ba. Inda ya bayyana cewa, Nijeriya ta fara aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana tun a shekarar 2014 inda aka fara aikin farko a jihohin Lagos, Kaduna da kuma Borno.

Ya ƙara da cewa, wannan tallafi da Birtaniya ta bayar zai ba wa kamfanoni masu zaman kansu da ma wajen shiga harkar samar da lantarki ta wasu hanyoyin. Kuma ya ba da tabbacin za a kasafta da kuɗin yadda ya dace.