Daga AMINA YUSUF ALI
A halin yanzu dai ana tsammanin rassa goma sha uku ne daga rassan Bankin Standard Chartered ne za su cigaba da aiki a ƙasar Nijeriya. Hakan ta faru a dalilin yunƙurin bankin na ganin ya rage wasu sassansa da ke ƙasar nan.
Shi dai wannan Rukunin Bankunan na Standard Chartered na Nijeriya yana da Shalkwatarsa ne a birnin Landan ta ƙasar Ingila. Babban banki ne wanda yake tafiyar da harkokin kasuwancin kuɗi iri daban-daban.
Jaridar Bloomberg ita ta yi wannan rahoto a ranar Litinin ɗin nan da ta gabata. Inda ta bayyana cewa, bankin zai dakatar da kaso 50 ko kuma rabin dukkan hada-hadarsa a rassansa na Nijeriya. Kuma a cewar majiyar tamu hakan ta faru ne sakamakon yunƙurin bankin na ganin ya sayar da wasu hannayen jarinsa da kuma cigaba da hada-hadarsa ta hanyoyin fasahar zamani, a cewar wasu makusantan hukumar bankin.
Tun a watan Disambar 2021 ne dai da ma suka dakatar da rassa 13 daga rassan bankin guda 25 a Nijeriya.
Lamin Manjang, manajan darakta na Bankin Standard Chartered ɗin a Nijeriya ya bayyana cewa shi ma bankin nasu zai shiga sahun sauran kamfanonin ba da rance da suke cin kasuwarsu ta hanyar manhajojin yanar gizo. Kuma zai goga kafaɗa da su domin harkar akwai gasa sosai.
Ya ƙara da cewa, bankin nasu a yanzu haka yana kan ƙara bunƙasa harkokinsa da kuma samun ƙarin kwastomominsa waɗanda a yanzu zai sakaya sunayensu.
Bincike ya nuna cewa, bankuna da dama har ma da manyan kamfanonin ba da rance suna ganin harkar ba da rancen a matsayin wata hanyar kasuwanci mai sauƙin kashe kuɗi wacce za a iya amfani da ita don kusantar ƙananan garuruwan karkara inda suke fama da qarancin (tallafin) kuɗi.