An rufe kasuwanni a Jihar Oyo saboda rasuwar basarake

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar litinin ɗin da ta gabata ne dai aka tashi da umarnin a rufe dukkan kasuwanni a jihar Oyo domin nuna girmamawa da alhini ga rasuwar Sarkin Ibadan ta jihar Oyo, (Olubadan); Oba Saliu Adetunji.

Wannan umarni na rufe dukkan kasuwannin faɗin jihar ya fito ne daga babban shugaban kasuwanni na jihar ta Oyo, Asiwaju Yekini Abass wanda aka fi sani da YK Abass.

Umarnin ya biyo bayan wani taron gaggawa na shugabannin kasuwanni na jihar da babban shugaban kasuwannin, YK Abass ya kira a ranar Lahadin da ta gabata. Wato jim kaɗan bayan mutuwar Basaraken.

Abass ya bayyana cewa, an yanke hukuncin ba da umarnin rufe kasuwannin ne domin a nuna alhinin mutuwarsa da kuma nuna girmamamawa ga Basaraken dangane da irin gudunmowar da ya bayar don cigaba a garin Ibadan da kuma Jihar gabaɗaya.

Sarkin na ƙasar Yarabawa, Olubadan Saliu, ya rasu ne ranar Lahadin da ta gabata. Kuma ya rasu yana da shekaru 93 a Duniya.