Har yanzu dai ta na jika kan batun matsalolin aure!

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Jama’a Assalamu Alaikum. Ina neman afuwa da dogon lokaci da na ɗauka ba a ji ni ba, rai da jini. Ga mu yau ma cikin filinmu mai albarka, filin tarbiyya.

Har yau dai ba ta sake zani ba! Muna cikin yanayi na matsalolin na yadda auratayya take tafiya a wannan zamani. Har yanzu muna cin karo da matsalolin auratayya na yaranmu dake faman rushewa kamar wutar daji, wanda kullum kukan iyaye dai wannan matsalar. Ni a iya kaina na ci karo da wannan kyasa-kyasan fiye da ashirin wallahi cikin sati biyu kacal.

Ya ilahil alamina! daga ina muka yi kuskure ne? Idan an ce tarbiyya sai na ga iyaye na ƙoƙari iya iyawa, amma abubuwan yaranmu na daɗa taɓarɓarewa. Na kan yi tunanin wai me yaranmu suke son mai da iyaye ne da kansu? Duk burin iyaye su ba wa yaransu tarbiyya, su zama nagari, abun alfahari. Su kuma yaran ba haka ne cikin zuciyarsu ba. Hasali ma nunawa suke yi sun fi iyayen wayo da dabara.

Yaro zai zauna ya tsara wa iyaye zance kamar gaske, ita kuma uwa saboda soyayya da ganin cewa ta riga ta ba wa yaranta kulawa da tarbiyya, ba za su yi abu mara kyau ba, sai sun aikata ta zo tana mamakin yaya haka?

A tunanina, shi da ma ɗa ba za ka ba shi yarda gabaɗaya ba. Saboda ba tare da shi kake rayuwa koyaushe ba. Dole sai kana binsa da idanu, nasiha da takurawa, yadda zai san koyaushe akwai mai kula da al’amuransa, sai a zauna lafiya.

Auratayya ta zama abinda ta zama yanzu kashi ɗari cikin ma’aurata bai fi kashi talatin ba yanzu suke zaune lafiya a gidan mazajensu ba. Wallahi ko’ina ka taɓa, babu daɗi fa. Idan uwa na son ɗiyarta ta yi zaman aure, to ta shirya tallafa mata ta ko’ina. idan na ce ko’ina, ina nufin ta kowanne ɓangare.

Duba da yadda auratayya yanzu ta koma, to sai uwa ta shirya raba dai-dai da mijin ɗiyarta. Wato ta fannin buƙatunta. Wallahi don ba zai iya yi mata hidima ba idan ba jarumin gaske aka samu ba. Idan ba ki shirya ba, to kullum ki tanadi hankicin goge hawaye, kawo ƙara ma kawai ya ishe ki.

Sana’a: tilas uwa ta koya wa ‘yarta yadda za ta nemi kuxi ko don uzirinta. Don mazan yanzu ba su san wannan ba.  Idan an samu ma ya ba ta abinci da sauran abun da ba a rasa ba, to ta gode wa Allah, domin ya yi mata kirki ma. wani ma abin da za ta ci ma sai lokaci lokaci idan ba za ki iya ba, ki ƙara gaba. Yanzu iyaye ke bautar yaransu a gidan mazan aure. Idan har ana so a zauna, kar a sako ta kenan. Samari na yanzu dake dagewa a yi musu aure to wallahi duk sha’awa ce. Da zarar an shiga an gama amarci, sai gayya ta watse ya fara fito mata da tsabagen wautarsa ta bai ma san meye auren ba.

Kowa sai ya gane kowa, sai tsana da hantara. Ko da za a zauna ɗin, to fa sai an yi da gaske. Mace sai ta rarrashi zuciyarta ta daina hasasshen waccan soyayya da ya nuna mata a waje, idan ba ita ba sai rijiya. Ba wannan maganar Kam. Ki kawo tsumma ki danne zuciyarki. Idan ba zai samu ba, nannaga wa zuciyarki dutse don abin ya fi ƙarfin magana sai ido da haƙuri. Idan ba Haka ba, to biyu babu za ki yi. Ba tsuntsu, ba tarko.

Uwa: Ita uwa, ita ya kamata  ta koya wa ɗiyarta yadda za ta yi zaman aure, ba sai lokaci ya ƙure ba. Yadda muke samun wayon yara na yanzu, daga shekara sha biyu ma yarinya za ta iya zaman aure ta yi daram a gidan ta ba tare da an ji kanta da mijin nata ba. To mu iyaye mata mu dage da koya wa yaranmu yadda za su zauna da miji, uwar miji, dangin miji, da sauransu. Idan ta haddace, magana ta ƙare komai zai zo mata da sauƙi. 

Sannan ta san ba buƙatar ta ce yadda ake mata a gida ko shi mijin yake mata a waje, idan ta shiga haka zai cigaba. A’a, da sauƙi dai ba zai yi ba, ba lokacin ma. Za ta ga canji ba na wasa ba, wallahi.

Hidima ta ƙaru a kansa, ta yaya zai samo musu abin buƙata a gidan? Ke kina ta a ci daɗi ina! Wannan zamanin kin yi sallama da shi lokaci ne na taimaka wa juna, ku inganta rayuwarku. Ku zauna zaman haƙuri, da yarda da juna, ku tsara rayuwarku dai-dai gwargwadon ɗauka.

Iyaye: ku daure ku dinga nusar da yaranku abubuwan zamtakewar aure a yanzu. Wallahi idan ba haka ba, wata ɗaya, biyu za ki ga ɗiyarki a gabanki. Muddin ta tafi da aƙidar komai sai miji ya yi mata, kamar tana gida. Ko ta hango gidan ƙawarta tana da kaza, ita ma sai nata mijin ya yi, to akwai daru.

Ɗabi’ar fa da yaranmu yanzu suka sa a gaba, gasa. Duk abinda aka yi wa ƙawarsu, to ita ma sai an mata hakan. Ba zai yiwu ba gaskiya. Idan ba shi da shi fa? Ko kuma shi ba mai yi ba ne, duk yadda za ki yi masa, wallahi ba zai yi ba. Gwara kin koyi haƙuri da ɗauke kai a kan abinda ba zai yiwu ba. Idan kin dasa shi cikin zuciyarki kuma, to ke ce a wahale.

Iyaye dukkansu: Iyaye su ringa nusar da yaransu maza, ba wai soyayya ce kawai zaman aure ba. Akwai haƙƙoƙi da yawa da suka rataya a wuyan magidanci da zai wa matarsa kamar yadda ka amshi aurenta gurin waliyyanta. Akwai sharruɗan ciyarwa, tufatarwa, magani, da duk wasu buƙqatunta na yau da kullum. Amma idan ba su saɓa wa addini ba.

To waɗannan abubuwan ma yanzu na ga mazan ba sa ɗauka. Sai su ce ba za su yi ba, ko ba su da shi. Ya ilahi! to ina za ta je a ba ta?

Da akwai aiki gabanmu fa a wannan marra. Dukkanmu kowa ya san rayuwa ta canza, ga matan sun yi yawa ba aure. A cewar mazan, suna so buƙatun da ake wa neman auren ne ya sa ba sa zuwa. Ko kuma suna zuwa amma ba da sigar auren ba, sai yaudara. Hakan kuma ta faru ne a kan rashin kuɗin auren. Daga nan fitina ta samu zama da kanta. Saboda duk sun kai munzalin auren, amma rashi ya hana. Kun ga an ɓata  goma, ɗaya ba ta gyaru ba.

Yawan zance ba neman aure ma yanzu turba ce ta saka yaranmu cikin fitina. Zuwa ya wuce uku, biyar, to za a samu matsala, wallahi. Gwara in da gaske ne, to iyaye su shiga lamarin.

Haka nan rashin haƙuri na ɗaya daga cikin dalilan taɓarɓarewar aure. Abunda ke damun kowa yanzu yadda ake kawo mata wankan haihuwa, daga nan sai a ajiye wa iyaye ɗawainiya. Ba ruwansa da duk hakkin da ya san nasa ne. Su ma iyayensa sai su yi ƙemadagas, su yi shiru su sa wa dangin mata ido. Wannan zalunci ne, wallahi. Kuma rashin sanin ƙimar ɗan da aka haifa ne. Da zarar ɗan ya girma, uba sai ya ƙeƙasa ido ya ce ɗansa ne. Har ma ya fi uwar iko. Ya manta sanda ya bar ta da ɗawainiyar yaron.

Mu mutunta juna, sai aure yayi inganci. Amma idan an sa son rai, komai ba zai zo yadda ake so ba. Duk yi wa kai ne. Don Allah iyaye mu lura da dukkan halayyar da yaranmu ke ciki. Idan sun kauce, a dawo da su hanya. Duniyar Allah faɗi gare ta. Muddin muna so mu ga da kyau, to mu yi abunda ya kamata.

Idan iyaye sun amince da yi wa yaransu aure, daga shekara ashirin da huɗu, a ce namiji zai iya riqe gida. Sannan Uba ya zaunar da yaro ya yi masa huɗuba da gargaɗi. Kuma ya nusar da shi zaman auren, da yadda ake yi. Ba wai a sa masa ido kawai a kai masa matar ba, a yi ta kwaɓa a gidan auren.

Haka ita ma macen, sai uwa ta yi mata karatun komai yadda za ta yi. A yi ƙoƙarin koya mata girki, gyaran gida, gyaran jiki, tsaftace madafi da makwanci, iya tattalin dukiyar miji, haƙuri da kau da kai, to kowa lafiya zai zauna. Amma muddin ba a koya mata waɗannan abubuwam ba, to aiki ya dawo baya. Abin da muka yi na daidai Allah ya amsa mana, ya shirya mana zuri’a, ya arzurtamu da zuri’a mai kyau. Ya raba mu da aikin da-na-sani.

Insha’Allahu sati mai zuwa za mu taɓo wani fanni mai mahimmanci. Ku kasance da mu cikin jaridarku mai farin jini, Manhaja. Ma’asallam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *