Barace-baracen ƙananan yara a tituna abin dubawa ne

Ga duk mai dubi zuwa ga yadda aka jefa ƙananan Yara cikin harkar barace- barace, musamman a biranen ƙasar nan zai ga cewa akwai sosar zuciya mutaƙa, musamman ganin yadda yaran ke fama da wahala, sannan ga ɓata sunan Hausawa da abin ke jawowa.

Akwai abubuwa da dama, waɗanda idan mutum ya yi dubi zuwa garesu za su dagula masa rayuwa ya ma rasa abin da ke masa daɗi, musamman idan aka duba yadda wasu abubuwa ke jawo wa rayuwar al’ummar da abin ya shafa.

Wasu daga cikin waɗannan abubuwa, waɗanda kuma za mu iya cewa babu wani mai farin ciki da shi, shi ne yadda ake samun ƙananan yara masu ƙananan shekaru suna bara a kan tituna, musamman a wasu manyan garuruwan ƙasar nan.

Irin waɗannan yara masu barace-barace suna nan birjik a manya da ƙananan garuruwanmu, suna bara ta hanyoyi da dama, wasu suna tare da iyayensu ne kamar ’yan jagora, idan iyayen makafi ne, wasu kuma iyayen almajiran ne, don haka su ma suke cikin bara, wasu kuma almajirai ne da aka tura wasu garuruwan da ba nasu ba domin yin karatun allo.

Irin waɗanan yara, wasu lokuta ma za ka tarar da cewa ƙanana ne matuƙa, ta yadda in da suna gidan iyayensu ne, kuma iyayen suna san abin da suke, hatta wanki ko wanka ma sai an yi masu, wasu ma ba su wuce kwana da iyayensu mata a gado ɗaya ba.

To amma abin takaici sai ya zama an raba su da iyayen nasu an jefa su bariki, ba abin da suke yi sai bara, babu karatun addini balle na zamani. Su kuma waɗanda suke karatun allo daga cikinsu, yunwa da rashin ƙoshin kafiya ma ta ishe su. Idan suna cikin wannan yanayi, wa zai yi masu wanka, wa zai yi masu wanki da sauran hidindimu?

A duk lokacin da na ga ririn waɗannan yara na kan tausaya masu, kuma na kan tausaya wa iyayensu. Ina tausayin yaran ne bisa mummunan halin da aka jefa su na azabar rayuwa, sannan su kuma iyayen ina tausayinsu saboda wannan tamkar sun yi watsi da amanar da Allah ya ba su ne, kuma tabbas Allah zai tambayesu amanar da ya ba su a gobe ƙiyama.

Sannan wani abin ban tsoro a irin waɗannan yara ake turawa cikin wannan mummunan hali, shi ne gurbataciyar tarbiyyar da suke tashi da ita. Domin ba sa samun tarbiyya ta gari, ba samun mai kwaɓa masu, irinsu ke tashi cikin mutanen nan masu aikta miyagun ayyuka.

Ba zan taɓa mantawa ba wani lokaci a kwanakin baya na ci karo da wani bidiyo da aka watsa a Soshiyal Mediya, inda aka nuna wani ƙaramin yaro, dududu bai wuce shekara biyar ba, ɗan jagora ne wanda ke ja wa mahaifinsa gora. Ga shi nan cikin mummunar shiga cikin datti zaune kusa da uban, amma ƙararamin yaron nan yana zuƙar siyari abinsa.

Wannan abu ya tayar mani da hankali matuqa. Domin shi mahaifin ba gani yake yi ba, in ma ya ji warin sigarin, in har ya tambaya, yaron zai iya ce masa ba shi ba ne, wani ne a kusa da shi ne, wa ya sani ma ƙila ko shi ma makahon mahaifin nasa yana sha ne har yaron ya koya?

Haka kuma irin waɗannan yara su suke tashi a ƙungiyoyin miyagun mutanen nan masu aikata miyagun ayyuka, ko kuma cikin waɗanda ake amfani da su wajen cimma munanan burace-burace na miyagun ’yan siyasar nan da ba sa ma kansu da al’ummarsu fatan alhairi.

Haka kuma a duk lokacin da aka samu wata hatsaniya, ta siyasa ce ta addini, to za ka tarar da irin waɗannan yara ne a sahun gaba wajen aiwatar da miyagun ayyuka. Su ne wajen kashe-kashen da ba hankali, sace-sacen kayan jama’a da ƙone masu dukiya, da dai sauran wasu munanan ayyuka.

A irin wannan ne wata rana aka yi kicibis da wasu yara maƙale da ɗan kwanonsu wai suna bara. Waɗannan yara, yara ne ƙanana, waɗanda idan da kai ne mahaifinsu, ko ke ce mahaifiyarsu, ba za ku iya sa su kowane irin aiki ba.

A batun gaskiya irin waɗannan yara masu irin waɗannan shekaru kamata ya yi a ce suna zaune tare da iyayeynsu suna zuwa makarantar Islamiyya da ta boko. Domin shi karatu irin wannan, yaro na gaban iyayensa ma zai fi mayar da hankali, musamman domin yana samun kulawa.

Idan aka rinka kwasar irin waɗannan yara ana turasu wasu garuruwa da sunan wai karatun allo, to wane irin karatu ne waɗannan yara za su yi, waɗanda hatta abincin kirki bai ishesu ba? Ya ake son su yi rayuwarsu, ya ake ganin tasowarsu za ta kasance?

Idan duk aka je aka dawo za a taras da cewa waɗannan matsaloli ne da suka dabaibaye Arewa, abin takaici! Kuma yawanci ana fakewa ne da addini, sai a ce wai yaro zai tafi neman ilimin addini, alhali ga yara nan suna haddace Alƙur’ani mai girma a gaban iyayensu, suna zuwa makaranta su dawo gidajensu ana lura da lafiya da tarbiyyarsu.

Shi kuwa wancan an tura shi wani gari an haɗa shi da wasu, ba uwa ba uba, Malaminsu, wanda shi kuma yaran sun yi masa yawa, wasu lokuta ma yaran kan faɗa cikin wani mawiyacin hali, ko ya kwashi wasu miyagun halaye, shi Malamin bai ma sani ba.

A matsayinmu na ’yan jarida mun sha cin karo da irin waɗannan matsaloli da dama, na sha samun labarai masu baƙanta rai game da irin halayen da waɗannan yara kan shiga, wanda wasu labaran ma ba a iya yaɗa su saboda takaicin da ke ciki. Domin akwai wani lokaci da ake samun yanayin da ake kama irin yara da aikata miyagun abubuwa, hatta luwaɗi.

Saboda haka ne Manhaja ke ganin wannan aiki ne da ya rataya a wiyan kowa, musamman iyaye, gwamnati da shugabannin al’umma. Domin ita tarbiyya ta kowa da kowa ce, idan ta gyaru, to al’umma ce za ta ji daɗi, idan kuma ta lalace, to al’umma ce za ta kwashi kashinta a hannu.

Wasu Gwamnoni a jihohin Arewacin ƙasar nan, musamman jihar Kaduna sun yi yunƙurin hana waɗannan abubuwa, amma saboda rashin samun goyon bayan al’umma, abin ya gagara. Domin idan suka cika matsawa sai a ce Gwamna wane yana yaƙi da addini, wanda kuma abin sam ba haka yake ba. Addini daban, waɗannan abubuwa kuma daban.