Babu ɗan siyasar da ya taimaki Kannywood kamar Sanata Barau – Sani Indomie

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A daidai lokacin da guguwar siyasar 2023 ta fara kaɗawa, su ma’ yan fim da su ke shiga harkar siyasa sun fara motsi domin ganin harkar ba ta bar su a baya ba. Sani Ali Abubakar, wanda aka fi sani da Furodusa Sani Indomie yana ɗaya daga cikin ‘yan fim da su ke shiga harkar siyasa, don haka ne mu ka ji ta bakin sa kan irin matakin da za su ɗauka dangane da zave mai zuwa don ganin sun samar wa da masana’antar cigaban da a ke buƙata, in da ya fara da cewar.

“To da farko dai harkar siyasa a wajen ‘yan fim ba wani sabon abu ba ne da suka fara a yanzu, domin kuwa tsawon lokaci an gano cewar ɗan fim zai iya bayar da gudunmawa a cikin harkar siyasa. Domin tun daga lokacin marigayi Rabilu Musa Ɗan Ibro, da ya shiga aka fara da shi.

Ko da ya ke kafin shi akwai Hamisu Lamiɗo Iyantama wanda shi har takarar gwamna ya yi a Kano, don haka dai su ‘yan siyasar sun yarda ‘yan fim da mawaƙa za su iya ba su gudunmawa don haka aka yi auratayya tsakanin ‘yan fim da ‘yan siyasa, kuma Allah ya sani dawowar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso gwamna karo na biyu, ‘yan fim sun bada gudunmawa kaso 40 cikin 100,don haka tun daga wannan lokacin aka gano ‘yan fim suna da tasiri a cikin tafiyar siyasa, wannan ya sa zai yi wuya ka ga ‘yan siyasa ba tare da ‘yan fim ba.”

Dangane da rarrabuwar kan da su ke da shi kuwa wanda a ke ganin hakan ya hana su cin gajiyar siyasar kuwa cewa ya yi, “Babu maganar rabuwar kai a tsakanin mu in dai tafiyar siyasa ce, domin kowa yana da na sa ra’ayin kamar yadda kowanne mutum ya ke da ra’ayin sa a cikin kowacce sana’ar, don haka kowa da akwai na sa ra’ayin a cikin tafiyar siyasar, domin idan ka ɗauka a yanzu manyan jam’iyyu a Nijeriya guda biyu ne APC da PDP.

To a yanzu akwai wanda ba ya yin su kuma ɗan fim ne, don haka mu ma mutane ne kamar kowa, muna da ra’ayi a cikin tafiyar siyasa daman haka abin ya ke, wani ɗan takarar ya ke yi, wani kuma jam’iyyar ya ke yi, don haka wanda ya ke bin ɗan takara zai iya tafiya kowacce jam’iyyar, idan kuma jam’iyya ka ke yi, ka ga ba kowanne ɗan takara za ka yi ba, don haka mutane ne su ke kallon abin ta wata fuska, amma a gaskiya ra’ayi ne, kamar ni a nawa ra’ayin a Nijeriya a waccan lokacin na zaɓi Muhammadu Buhari, kuma ko gobe ya fito zan zave shi. Amma ka ga ra’ayin wani ba haka ba ne, sannan a nan Jihar Kano a yanzu Barau I Jibrin Maliya shi na ke yi.

Amma a waccan zaɓen, ina Buhari a sama a Kano kuma Muhammadu Abacha na yi, kuma in banda a yanzu tun da na ke siyasa ban taɓa sauya ɗan takara ba a Kano sai Muhammadu Abacha, amma yau sai ga shi a tafiya ta ina yin Barau I Jibrin, ka ga ai ra’ayi ne, don haka kullum abin da mu ke dubawa Menene cancantar mutum waye kai, me za ka taimaki jama’a da shi, domin maganar gaskiya ni Kano ce a gaba na, waye zai taimake mu da sana’ar mu? Saboda kullum kwanakin mu tafiya su ke yi, don haka a yanzu na ke tafiyar Barau Jibrin don zai taimaki masana’antar mu da jihar mu.”

Ya ƙara da cewar, “a yanzu Ina tabbatar ma ka da cewa duk wani ɗan siyasa babu wani Mutum da ya taimaki masu harkar fim kamar Barau I Jibrin saboda tun da ‘yan fim suke idan har an taɓa ba su tallafi, to gaskiya ba mu sani ba a ce ɗan siyasa ya ɗakko wani tallafi ya bai wa ‘yan fim wanda sama da dubu suka samu, domin a cikin ‘yan ƙungiyoyi da kamfanoni an raba musu tallafi daga mota zuwa babur da kwamfuyuta, da kuɗaɗe, to ka ga wannan ya nuna za mu samu cigaba a masana’antar mu idan har Allah ya sa ya samu nasara.”

Daga ƙarshe ya yi godiya ta musamman ga Alhaji Murtala Alasan Zainawa da Isiyaku Abubakar Balan, saboda gudunmawa da suke bayarwa wajen samun tallafin da a ke yi wa ‘yan fim sannan ya yi kira ga’ yan fim da su tsaya don Allah su zaɓi wanda ya cancanta wanda za mu je masa da maganar masana’antar mu kuma ya taimake mu, saboda ba mu da wata sana’ar da ta fi harkar fim.

Saboda a baya akwai na mu da su ka je sama a siyasance, amma ba su taimaki masana’antar ba, har ma wasu sun yi ƙoƙarin su kore mu daga Kano, wasu ma sai ka ga kamar kwangilar rusa masana’antar aka ba su da suka samu sama a siyasar don haka mu haɗa kan mu mu nema a wajen Allah mu zaɓi wanda zai samar mana da cigaba wanda idan mu ka je da kukan mu zai saurare mu.