ECOWAS ta ba wa Najeriya mafita kan tafiyar hawainiya a sashen noma

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban sashen harkar noma na gamayyar ƙungiyoyin Afirka ta Yamma (ECOWAS), Dakta Ernest Aubee ya yi kira ga Nijeriya da ta magance tafiyar hawainiyar da sashen noma yake yi a ƙasar.

A cewar Ernest Aubee, wannan shi ne kaɗai abinda zai kawo mafita a kan matsalolin da suke kewaye da fataucin hatsin da ƙasar ta noma a tsakaninta da ƙasashen yankin na Afirka ta Yamma.

Wasu daga cikin matsalolin da a cewar sa auke kawo cikas sun haɗa da, jinkirta motocin kayan abincin daga shiga bodar wasu ƙasashen, biyan maƙudan kuɗaɗen da ake yi kafin a bari a shiga da kaya ko a fita da su zuwa wasu ƙasashen, da kuma yin buris da yarjejeniya da ƙasashe mambobin ECOWAS suka yi na ‘yancin shige da fice na mutane ko kaya a tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma, sannan da karya dokar kyautata hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen da suke mambobi a ECOWAS ɗin.

Dakta Aubee ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai a garin Abuja.

A halin yanzu dai a cewar sa, Njeriya ita ce ƙasar da take samar da kaso 50 daga cikin hatsin da ake fataucinsa izuwa ƙasashen Afirka ta Yamman. Amma yanzu hakan na nema ya gagara duk da yadda ECOWAS ɗin ta shimfiɗa dokokin da za su taimaka wajen bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen na Afirka ta Yamma.

A cewar sa, ba wata mafita da ta wuce ƙasashen su yi biyayya ga shimfiɗaɗɗen tsarin da ECOWAS ta samar na kasuwanci tsakanin ƙasashen. A cewar sa, rashin samun shamaki ko jinkiri wajen fataucin hatsin shi ne babban abinda zai bunƙasa harkar fataucin hatsin.

Sannan kuma a cewar sa, ECOWAS tana daga cikin hukumomin da suke da burin ganin an samu sauƙi a wajen wadatar da ƙasashen da hatsi.

Hukumar cigaban ƙasashen waje ta ƙasar Amurka (USAID) tare da haɗin gwiwa da hukumar bincike da bunƙasa harkar noma ta Afirka, (CORAF) tana nan tana shiryar da gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki domin a samar da wani tsari da zai samar da yanayi mai kyau don tabbatar da shige da ficen hatsi a tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *