…Bayan Malami ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
A wani yanayi na kawo tarnaƙi ga ƙoƙarin da Shugaban Nijeriya Muhammadu ke yi wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaron ƙasar, musamman ma ’yan bindiga, waɗanda suka suka warwatsu a faɗin ƙasar suna yi wa ’yan Nijeriya kisan kiyashi, Gwamnatin Amurka ta yi barazana ga Shugaba Buharin kan amfani da fitaccen jirgin yaƙin nan da ta sayar wa Nijeriya na Super Tucano (Tukano) a kan ’yan bindigar bayan da Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya sanar da ayyana su ’yan bindigar a matsayin ’yan ta’adda.
Gwamnatin ta Amurka ta jaddada wannan matsayin nata a wata sanarwa da ofishin jakadancinta ya bayar Alhamis da ta gabata, ta na mai cewa, dole ne amfani da jirgin yaƙin ya dace da ƙa’idojin ƙasashen duniya da yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya, wacce ta hana amfani da irin jirage kan masu aikata laifukan da bas u shafi ayyukan ta’addanci ba. Don haka sai Amurkan ta ja kunnen Shugaba Buhari kan wuce gona da iri a yayin amfani da shi, musamman wajen yaƙar ayyukan laifukan da ta kira da na al’ada a cikin gida.
Duk da cewa, ƙasar ta Amurka ta kuma yarda da cewa, tabbas Nijeriya ta na fuskantar ƙalubalen tsaro a cikin gida, amma sai ta yi gargaɗi ga Gwamnatin Nijeriya da sojojin ƙasar wajen wuce gona da iri a yunƙurin da Shugaban Ƙasar ke yi wajen fuskantar wannan ƙalubale, ta na mai cewa, dole ne a girmama ’yancin ɗan adam a yayin yaƙin.
A sanarwar da mai magana da yawun Amurka a ofishin jakadancinta da ke Abuja, Jeanne Clark, ya fitar a jiya, don mayar da martani kan iƙirarin Malami (SAN) na cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta samu amincewar yin amfani da jiragen Tukano da ta sayo daga Amurka bayan da kotu ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda, kamar Boko Haram, ISWAP da sauransu, ofishin jakadancin na Amurka ya ce, bai dace a yi amfani da jiragen ba tare da la’akari da ’yancin bil adama ba, musamman kan laifukan da suka zama an saba aikata su a cikin ƙasa.
Shi dai jirgin yaƙin Tukano shi ne jirgin da duniya ta ke yayinsu wajen yaƙi da ’yan ta’adda a ko’ina. Tun lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ƙasar ta nemi Amurka ta sayar ma ta da su, amma shugaban Amurka na wancan lokaci, Barack Obama, ya ƙi amincewa, saboda rashin amincewa da amanar tsohuwar gwamnatin Jonathan.
To, amma bayan zuwan Gwamnatin Buhari, Amurka ta amince ta sayar wa Nijeriya jiragen bisa amincewar Shugaban Amurka Joe Biden. Tuni Nijeriya ta amshi jiragen tun a tsakiyar shekarar 2021 da ta gabata, kuma har ta kammala horon sojojinta, don aiki da jiragen. Kai tsaye Nijeriya ta iya yaƙar Boko Haram da ISWAP da IPOB, saboda an daɗe da ayyana su a matsayin ’yan ta’adda, to amma rashin ayyana ’yan bindigar daji masu garkuwa da mutane ya sanya ba ta da ikon yaƙar su da jirgin bisa dogaro da yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sai dai kuma a cikin makon nan, wata Babbar Kotun Tarayya ta ayyana ’yan bindigar a matsayin ’yan ta’adda, lamarin da ya sanya Ministan Shari’a fitowa ya yi iƙirarin cewa, yanzu an share wa Shugaba Buhari hanyar amfani da wannan jirgi na musamman, don tarwatsa ’yan bindiga.
Katsam kuma a jiya Alhamis, 6 ga Janairu, 2022, sai ga wannan sanarwa ta Amurka, wacce ta ke nuna barazanarta ga Nijeriya.
A cewar sanarwar Amurka ta ce, “nazarinmu kan lamarin shine la’akari da cewa, sun a haifar da barazana ga zaman lafiyar tarayyar ƙasar kuma su na janyo babbar barazana ga rayuka ta hanyar amfani da makamai, don haka mu ke da tunanin cewa, su (’yan bindigar) sai sun cika dukkan wata ƙa’ida da za ta sa a ayyana su a matsayin ’yan ta’adda daidai da tsarin doka, domin sojoji su samu ikon yin amfani da dukkan makaman da Gwamnatin Tarayya ta mallaka a kan su bisa la’akari da yarjejeniyar ƙasashen duniya kuma daidai da doka.”
Daga nan kuma sai sanarwar ta yaba wa Nijeriya bisa yadda ta fara amfani da jirgin Tukano ƙirar A-29 Super Tucanos cikin nasara a kan ’yan Boko Haram da ISWAP.
Sai dai kuma duk da haka, wasu na kallon sanarwar ta Amurka a matsayin wata barazana da za ta iya haifar da koma-baya a ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi wajen shawo kan matsalolin tsaron da ’yan bindiga suke haifarwa a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda jihohi irin su Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Neja, Benuwe, Adamawa da sauransu ke fuskantar rashin zaman lafiya zaman ɗarɗar sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindigar daji da kuma masu yin garkuwa da mutane su na amsar kuɗin fansa.
Tun bayan zuwan Gwamnatin Shugaba Buhari a shekara ta 2015 ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC sai ya duƙufa wajen kashe maqudan kuɗi, domin kawo ƙarshen matsalolin tsaron ƙasar da a ke kallon cewa, su ne suka haifar da faɗuwar Gwamnatin Jonathan a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP.
To, amma kawo yanzu, daga dukkan alamu, wankin hula ya na neman kaiwa dare. Domin har yanzu matsalolin tsaron ba su gusa ba. Sai ma yadda wasu ke kallon cewa, al’amura sun sake taɓarɓarewa ne. Don haka ba abin mamaki ba ne, idan APC ta tashi tsaye wajen yin amfani da dukkan damar da ta ke da ita, musamman ta amfani da makamai na zamani, wajen ganin ta wabke kanta daga kallon da yawancin ’yan Nijeriya ke yi ma ta na gaza cika alƙawarin da ta ɗauka, saboda ganin yadda kakar babban zaɓen 2023 ta ƙaratowa.
To, amma irin wannan barazana daga manyan ƙasashe irin Amurka na daƙile su wajen amfani da makaman da suka dace, kamar Tukano, zai iya kaseh gwiwar gwamnatin.
Idan dai za a iya tunawa, a cikin littafin da tsohon Shugaba Jonathan ya rubuta mai suna ‘My Transition Hours’ ya kuma ƙaddamar da shi a watan Nuwamba na shekara ta 2018, ya yi zargin cewa, Amurka ta taka muhimminyar rawa wajen hana shi kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya a zamaninsa ta hanyar ƙin ba shi goyon baya da tallafin da suka kamata a lokacin yaƙi tare da ƙin sayar masa da makamai ingantattu, don kawai ta na so ya faɗi a babban zaɓen 2015, kuma hakan ce ta faru, domin ga shi daga bisani ta amince za ta sayarwa da Gwamnatin Buhari irin waɗannan makamai.
Tun bayan zuwan Buhari mulki dai aka fara tattauna tsakanin gwamnatinsa da ta Amurka, inda a shekara ta 2019 aka cimma yarjejeniyar sayen makamai a tsakaninus, kuma a shekara ta 2020 zuwa 2021 jirage suka fara iso wa Nijeriya.