Kaso 17.4% ne kawai na harajin 2021 ya shiga asusun Gwamnati – NNPC

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin Kula da man fetur, NNPC ya bayyana cewa, kaso 17.4 daga harajin da kamfanin ya tara a tsahon shekarar bara ne kawai ya shiga asususun kamfanin. Wato daga cikin kuɗaɗen da kamfanin ya tara Naira Tiriliyan 2.99, daga watan Janairu zuwa Nuwambar shekarar 2021. 

A cewar NNPC, dukka ragowar kuɗaɗen an ɓatar da su ne a garin biyan kuɗin tallafin mai da laluben man fetur ɗin da kuma tafiyar da wasu al’amura a kamfanin.

NNPC ta yi wannan bayani ne a cikin rahotonta ga kwamitin kula da asusun gwamnatin tarayya (FAAC) na watan Disamba wanda ta wallafa a turakarta ta yanar gizo a Larabar makon da ya gabata. Wanda jaridar Ripples Nigeria ta rawaito. 

Rahoton ya bayyna cewa, NNPC ta gudanar da wasu ayyuka guda 11 da suka lamushe Naira Triliyan 2.47 a tsakanin Watan Janairun da Nuwamba,  inda hukumar NNPC ta tsira da Naira Biliyan 522.20 kacal wanda za a yayyaga shi tsakanin matakai uku na mulkin ƙasar nan. Wato majalisar dokoki, da ta zartarwa da kuma shari’a. 

A cewar rahoton, tallafin mai shi ne abinda ya fi kowanne jan kuɗi. Inda ya lamushe har Naira tiriliyan 1.16 a cikin watanni 11 kacal.

Sauran abubuwan sun haɗa da bunqasa gas ɗin girki a cikin gida (Naira biliyan 42.4), sai bunƙasa kayan aikin samar da gas ɗin (biliyan 34.06), sai laluben man fetur (biliyan 30.22). 

Sannan kuma ɓangaren kula da tsaron bututun man fetur (Naira biliyan 45) da dai sauran tsarabe-tsarabe.