Bankin Duniya ga Nijeriya: Ku yanka wa mashaya taba, barasa da kayan zaƙi haraji

Daga AMINA YUSUF ALI

Bankin Duniya ya nemi Gwamnatin Nijeriya da ta yanka wa mashaya barasa da taba da sauran kayan sha na zaƙi haraji domin inganta lafiyar al’umma.

Daraktan ƙasa na Bankin Duniya a Nijeriya, Shubham Chaudhuri, shi ya bayyana haka a ranar Juma’ar da ta gabata. Inda ya ƙara da cewa, in dai har ana son inganta lafiyar ‘yan Nijeriya, dole a sanya musu haraji mai nauyi a kan shan abubuwan da aka san suna cutar da al’umma saboda tsananin illarsu ga lafiyar mutane. Hakan a cewar sa wata hanya ce ta ceto rayuwar dubban ‘yan Nijeriya daga halaka.

Chaudhuri ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’ar da ta gabata a taro na musamman na majlisar kiwon lafiya ta ƙasa, a Abuja. Wanda ma’aikatar lafiya ta Tarayya ta shirya.

A cewar sa, sanya harajin ba wai kawai lafiyar ‘yan Nijeriya zai inganta ba, har ma kuɗin shigar ƙasa zai ƙara bunƙasa, ta ƙara samun damar fita daga ƙangin talaucin da ta shiga bayan annobar COVID 19.

Sannan kuma a cewar sa, za a samu ragi daga kuɗaɗen da ƙasar take kashewa a kan harkar asibiti da kiwon lafiya. Sannan za a rage samuwar miyagun cututtuka kamar tarin shiƙa, da sauran cututtuka da shan giya da taba da kayan zaƙi suke haddasawa. Kuma za a rage yawan yaɗuwar su tsakanin al’umma. Sannan uwa uba za a samu sauƙin talauci a ƙasar.

Shi ma a nasa jawabin, wakilin ƙungiya lafiya ta Duniya mai zaman kanta (WHO), Dakta Walter Mulombo ya bayyana cewa, zai yi iya iyawarsa wajen ganin an fitar da Nijeriya daga matsalolin da suka shafi lafiya a ƙasar.

Sannan ya ƙara da cewa, tabbas annobar COVID-19 Ta yi illa matuƙa ga tattalin arzikin ƙasashen Duniya, don haka ya kamata kowacce ƙasa ta san dabarar da za ta yi domin magance ƙalubalen rugujewar tattalin arziki a ƙasar.

Kuma a ƙarshe, Walter Mulombo ya ƙara jaddada goyon bayan WHO ga Nijeriya da alƙawarin ba da dukkan wata gudunmowa da za ta ƙara bunƙasa da cigaban ƙasar.