‘Yan Nijeriya miliyan 109 ne za su faɗa talauci nan da 2022 – Ministar kuɗi

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Talatar da ta gabata ne, gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, jimillar adadin yawan matalautan Nijeriya zai kai miliyan 109 nan da ƙarshen shekara mai kamawa ta 2022.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ministar kuɗi da tsara kasafin kuɗin ƙasa, Zainab Ahmed ta bayyana cewa, adadin matalauta a Nijeriya zai tasamma miliyan 109 nan da ƙarshen shekarar baɗi. Inda ta ƙara da cewa, za a samu ƙarin wasu ‘yan Nijeriya da za su dulmiya a cikin talauci nan da ƙarshen 2022 a sakamakon lara ɓarkewar annobar cutar COVID-19 . Abinda zai kama jimlar yawan masu talauci a Nijeriya sun kai miliyan 109.

Ministar ta yi wannan jawabi ne a Birnin Tarayyar Abuja a wani taro a kan cutar Kwarona.

Ministar wadda Darakta Janar na ofishin kasafi na ƙasa, Ben Akabuezebya wakilta, ta bayyana cewa, kafin annobar Kwarona, masana sun yi hasashen ‘yan Nijeriya miliyan biyu ne kacal za su afka a talauci a 2020, amma sai ga shi an samu ƙarin mutane fiye da miliyan shida da rabi sun faɗa talauci. Abinda ya sa aka samu jimillar mutane fiye miliyan takwas da rabi da suka faɗa talauci.

Dalili kuwa, yawan ƙaruwar mutane ya ninka yawan ƙaruwar tattalin arziki a ƙasar. Don haka aka yi hasashen samun matalauta daga miliyan 90 zuwa miliyan 190 daga 2020 zuwa shekarar 2022.

Ministar ta zargi rashin aikin yi da rashin kuɗaɗen shiga a matsayin ummul aba’isin na ta’azzarar talauci a ƙasar nan.