FIRS ta tara Naira tiriliyan 4.2 a cikin wata tara kacal

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar tattara haraji ta tarayyar Njeriya (FIRS), ta bayyana cewa, ta tattara haraji da ya kai Naira tirilian hu]u da biliyan biyu a tsakanin watanni tara kacal. Wato tsakanin watan Janairu zuwa watan Satumbar shekaran nan ta 2021.

Shugaban zartarwa na hukumar tattara harajin, ta FIRS, Mista Mohammad Nami shi ya bayyana haka a yayin taron ranar FIRS ta musamman wato ranar baje-kolin kasuwancin ƙasa da ƙasa wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Jahar legas. 

Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa, Mohammad Nami ya ce, hukumar FIRS ta yi ƙoƙari wajen cimma tattara waɗancan maƙudan kuɗaɗen duk da ƙalubalen annobar cutar Covid19 da ƙasar ta fuskanta. 

Inda ta rawaito Nami yana cewa: “ina mai farin cikin sanar da dukkan mahalarta taron cewa, harajin da muke tattarwa ya ƙaru matuƙa. Duk da ƙalubLen da muka fuskanta daga annobar COVID-19.”

Ya ƙara da cewa: “Yanzu haka hukumar FIRS ta tara ku]in haraji Naira tiriliyan 4.2 a tsakanin watan Janairu da Satumbar 2021”. Kuma a cewar sa, wannan nasara ta samu da taimakon manhajar tattara haraji ta yanar gizo ta ‘TaxPro Max’. Har ma da sauran hada-hadar tattara haraji ta yanar gizo.

Kuma a cewar sa kafin nan kafin ƙarshen shekarar 2021 suna fata hukumar ta cimma hasashen gwamnatin tarayya na tattara Naira Tiriliyan bakwai da biliyan shida kafin nan kafin ƙarshen shekarar 2021.