Ba sai da wayar Andiroi ‘yan Nijeriya za su iya hada-hadar eNaira ba – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Nijeriya, CBN ya bayyana cewa, ba fa sai da wayar andiroyi ko da yanar gizo ‘yan Najeriya za su iya yin hada-hadar kuɗi na eNaira ba.

Ita dai eNaira kamar yadda Babban Bankin ya bayyana cewa, shi ma tsari ne kamar sauran tsarin hada-hadar kuɗi ta yanar gizo ko manhajojin hada-hadar kuɗi na kan waya da muke da su da ma. 

Inda ya ƙara da cewa, tsarin zai ƙara wa ‘yan Najeriya sauƙin hada-hadar banki tare da faɗaɗa shi. Domin za a dinga hada-hadar ba tare da sayen data don shiga yanar gizo ba. Hasali ma dai har wayar salular da ba ta da yanar gizo za a iya amfani da ita wajen hada-hadar. 

Don haka yanzu, harkar banki za ta zama ba ta da gefe ga kowa. Musamman mutanen da suke ganin an yi musu nisa ko an wuce da su wato kamar marasa ilimi, ko marasa wayewa ga na’urori da fasahar zamani. 

A cewar CBN akwai kaso mai yawa na waɗancan rukunin mutane marasa karatu da marasa wayewa kuma shi CBN ba zai iya kasadar ƙyale su a baya ba, ba tare da ya janyo an tafi da su ba. Domin shi ma bankin yana buƙatar waɗancan mutane don su ƙarfafe shi. Shi ya sa aka samar da sabuwar fasahar hada-hadar kuɗi ta eNaira. Sannan kuma domin a sauƙaƙa wa al’umma mu’amalar kuɗi.