Kamfanonin MTN da Airtel sun samu lasisin gudanar aikin banki

Daga AMINA YUSUF ALI

Manyan kamfanonin sadarwar nan na MTN da Airtel sun samu lasisin tafiyar da harkokin banki da hada-hadar kuɗi a Nijeriya.

Shi dai kamfanin MTN, wanda ya mamaye kaso 40 na kasuwar sadarwa a ƙasar, da kuma Airtel, wanda ya mamaye kaso 27, sun samu sahalewar Babban Bankin Nijeriya (CBN), domin su fara tafiyar da harkokin banki a faɗin ƙasar, kamar yadda jiga-jigan  kamfanonin sadarwar guda biyu suka bayyana a ranar Juma’ar da ta gabata. 

Kamfanonin sun bayyana hakan a wasu takardu mabanbanta da kamfanonin sadarwar suka aike wa da hukumar canji ta ƙasar Nijeriya. 

Shi dai kamfanin Airtel babban kamfanin sadarwa ne da hada- hadar kuɗi wanda ya kafu kuma yake gudanar da harkokinsa a ƙasashen Duniya guda goma sha huɗu.

A ta bakin shugaban kamfanin, Segun Ogunsanya, Ya bayyana a cikin wasiƙar  cewa, Nijeriya ma ta shiga sahun sauran ƙasashen da aka lamunce musu su gudanar da hada-hadar kuɗaɗensu a ciki.

Inda ya ƙara da cewa, kamfanonin guda biyu za su samu cikakken lasisin bayan sun cikasa wasu sharuɗɗa nan da watanni shida masu zuwa. Sannan kuma za su yi aiki tare da CBN domin cimma manufarsu.
Shi kuma a nasa ɓangaren, Kamfanin sadarwa na MTN, shi ma ya bayyana a tasa takardar cewa, ya samu sahalewar Babban Bankin Nijeriya (CBN) don yin harkar hada-hadar kuɗin a ranar 4 ga Nuwamba, 2021.

Inda su ma suka ambata cewa, wannan mataki ne na farko, kuma suna nan suna dakon samun cikakken lasisi bayan sun cikasa sauran sharuɗɗan da Bankin CBN yake buƙata. Kuma za su kasance masu biyayya da girmama tsarin CBN. 

Shi dai wannan lasisin bankin da aka ba wa kamfanonin sadarwar ana sa ran zai kawo gogayya da rige-rige tsakanin kamfanonin da bankuna wajen gudanar da aikinsu. Abinda ake sa ran zai kawo ci gaba da sauƙaƙawa a harkar banki da hada-hadar kuɗaɗe a faɗin ƙasar nan gabaɗaya.