Rushewar benaye da ban tsoro

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, ko a Legas da ke bakin teku babu inda ba a tava samun aukuwar rugujewar bene ba, kuma duk lokacin da irin wannan akasi ya auku sai an samu asarar rayuka. Wani lokacin za ka tarar mutanen da akasin ya rutsa da su na zaune ne a cikin benen da ba a kammala ba sai ya ruguje a kansu, inda a wani lokacin kuma ma’aikatan da ke aikin ginin ne hakan kan rutsa da su.

Na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a Ikoyi da ke Jihar Legas, inda benen da a ke kan aiki a kansa ya ruguzo kan mutane har ya rutsa da fiye da mutum 40. Ginin dai mai hawa 21 ya zama bigiren da ma’aikata da dama ke aiki, don samun kuxin shiga ciki ma har da labarin wata mai yi wa ƙasa hidima. Tuni wannan labari ya ja hankalin kafafen labaru da jami’an agaji.

An ga wani faifan bidiyo ma inda manyan jami’an gudanar da ginin ke tsaye a ƙololuwar ginin su na nuna farin cikin nasarar gina wannan dogon benen da ya juye zuwa sanadiyyar ajalin mutane.

Haƙiƙa da irin benayen nan ne masu hawa 3 zuwa 5 ko makamancin haka da kan ruguje bayan dakatar da aikin gini na wani lokaci, zai yi wuya nan take a iya gano bayanan waɗanda su ka mutu. Hakan ya kan faru ne don talakawa ko ‘yan share-waje zauna za su iya zama su na mazaunan waɗanda kuma ba a san su ko ma a ce masu ginin ba su san su ba ko ma ba su ba su izinin zama ba don kamar an jingine aiki ne da yiwuwar na wata gwamnati ce ko hukuma ko ma mai hannu da shuni da ba su damu da aikin ba tun da ba su saka a ka ba. Hakanan ƙaddara kan iya sa wani ya zo wucewa ko wata hidima ta kawo shi ta inda ginin ya ke sai a samu akasin a daidai lokacin har ya kai ga rasa rai. Lamarin ya sha bamban da ginin da ya rushe alhali a na kan aiki. Don haka za ka tarar kowa na wajen tsakanin talakawa da masu hannu da shuni ko a ce tsakanin leburori da injiniyoyi da sauran ƙwararru.

Hukumar agajin gaggawa ta Nijeriya ta bayyana cewa ta gano gawar shugaban kamfanin ‘FOURSCORE HOMES’ da ke gina benen nan mai haws 21 wanda ya ruguje a Ikoyi ya hallaka mutane da dama. Hukumar ta gano gawar mutumin mai suna Femi Osibona a aikin binciken gawarwakin mutanen da ginin ya ruguje a kan su.

Kamfanin na gina jerin benaye uku ne inda ɗaya ya ruguje yayin da yanzu haka biyu ke nan a tsaye. Gwamnan Legas Babajide Sanwo Olu ya kafa kwamitin bincike don gano dukkan bayanan yadda lamarin ya auku. Da farko dai aikin ceton mutanen kamar ba ya sauri amma daga bisani gwamnatin Legas ta turo ƙarin kayan aiki da ma’aikata; inda gwamna Olu kan ziyarci bigiren don yin bayanin cigaba da a ke samu. Mutum 50 ne a ke da tabbacin ginin ya ruguje a kansu.

Gwamnan ya dakatar da babban manajan hukumar kula da tsarin gine-gine na Jihar Mr.Gbolahan Oki. Gabanin dakatar da shi Mr.Oki ya ce, an ba wa mai ginin izinin gina hawa 15 amma sai ya zarce ya gina 21 da kuma amfani da kayan gini marasa inganci. Gwamnan bai tsaya a nan ba sai da ya qara da cewa, laifin ya shafi gwamnati da masu aikin ginin.

Hakan na nuna za a samu gwamnati da sakaci wajen batun ba da izini ko rashin zuba ido don tabbatar an tsaya kan ƙa’idar yawan hawan benen da kuma ingancin kayan da a ka yi amfani da su wajen gina benen. Su kuma masu gudanar da gini ba mamaki ba su bi ƙa’idar da a ka shunfuda ba ta yiwuwar yin haɗama da rashin tantance kayan aikin da su ka yi amfani da su. Koma dai me za a ce, wannan babban abun juyayi ne tun da ya haddasa asarar rayukan mutane da dama kuma ya ƙara dawo da fargabar cewa wasu daga dogayen gine-gine da a ke yi ka iya zama ba tare da bin ƙa’ida ba. Gwamna Olu ya nuna takaicin abun da ya auku da ya ke ganin ba daidai ne a wannan sabon zamani a samu gine-gine na rugujewa haka a Legas ba.

A na cikin batun ceto mutane sai ga wani labarin zargin ai filin ginin ma mallakar mataimakin shugaban Nijeriya Yemi Osinbanjo inda har a ka nuna mai gudanar da kwangilar wanda ya riga mu gidan gaskiya Femi Osibona xan barandar Osinbanjo wajen irin waɗannan ayyuka. Ofishin mataimakin shugaban ya yi watsi da labarin da nuna tsantsar sharri ne kawai. Kakakin mataimakin shugaban La’olu Akande ya ce Mr.Osinbajo ba shi da wata alaƙa da ginin don an bayyana duk dukiyar da ya mallaka. Bayanan na Akande na nuna mataimakin shugaban zai kai qarar waɗanda su ka wallafa labarin don bin kadun ƙage da a ka ma sa.

Tuni iyali 49 su ka bayyana cewa, akasin ya rutsa da ‘yan uwan su da wa imma sun gamu da ajali ko kuma a ce zuwa yanzu ba a ga wasun su ba. Zuwa rubuta wannan shafi na ALƘIBLA an gano gawar fiye da mutum 40 da tabbatar da kuɓutar mutum 15 har da waɗanda su ka samu rauni a cikin su. Gaskiya ba za a iya sanin haƙiƙanin abun da ya faru ba har wannan dogon gini ya rufta sai an fito da sahihin bincike daga kwamitin binciken da a ka ɗora wa alhakin hakan.

A duk lokacin da irin hakan ya auku, kwararru wajen gini kan yi sharhi kan dalilan. Akasarin abun da yafi fitowa fili shi ne rashin bin ƙa’ida ta ɓangaren wuce gona da iri na lafta yawan benaye da kuma rashin sanya ingantattun kayan gini da za su iya riƙe nauyin da a ka lafta mu su. Ai kamar mota ce duk girman ta ba za ta ɗauki yawan kayan da jirgi zai ɗauka ba hakanan kamar kaulin fasahar nan da ke cewa ƙarshen alewa ƙasa wato a nan duk tsawon ginin da a ka gina indai ba shi da inganci to ƙasar ce za ta sake ɗaukar nauyin kayan ta.

A na cikin wannan labari na juyayi a Legas sai can ma Freetown na Saliyo a ka samu labarin wata tanka shaqe da fetur ta yi taho mu gama da wata mota inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 99 yayin da 100 su ka samu raunuka. Hatsarin ya rutsa da masu neman ɗibar man fetur ne don samun na bulus.

Lokaci ya yi da mutane za su faɗaka cewa da zarar an ga irin wannan hatsari a guji neman kwasar ganima don ganimar ka iya zama ajali. Ina amfanin baɗi ba rai. Shawara dai a nan a guji rufawa kan motar fetur in ta yi hatsari, a bar wa ƙwararrun jami’ai su yi aikin su na ceto da hana tashin irin wannan gobara bal-bal.