13
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce yawan yara marasa zuwa makaranta a Nijeriya a barazana ce da ke buƙatar haɗin gwiwa daga dukkan matakan gwamnati da masu ruwa da tsaki. Shettima ya yi wannan bayani a taron Zauren Ilimin Nijeriya na 2025 da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya tare da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da abokan hulɗa suka shirya. Ya ce matsalar ilimi ba za ta iya warwarewa da ƙoƙarin gwamnati kaɗai ba, yana mai jaddada cewa: “Yawan yaran da ba sa zuwa makaranta buƙatar gaggawa ce ta ƙasa da…
