Ramadan: ‘Ku sassauta farashin kayan abinci’ — kiran Sarkin Kano, Ado-Bayero ga ‘yan kasuwa

Daga BASHIR ISAH

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su sauke farashin kayan abinci da sauransu domin bai wa al’umma damar yin azumin Ramadan cikin walwala.

Basaraken ya yi wannan kira ne a wajen taron ƙaddamar da littafi mai taken: “Dauloli a Ƙasar Hausa” wallafar Farfesa Sa’idu-Mohammed Gusau wanda ya gudana ranar Lahadi a Zaria.

Kazalika, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su dubi Allah su taimaka wa mabuƙata yayin watan na Ramadan.

Ado Bayero ya yaba wa marubucin littafin bisa ƙoƙarin da ya yi wajen bayyana Masarautun Hausa da ke Kano, Katsina, Zamfara, Kebbi, Zazzau da sauransu a cikin littafin nasa.

A nasa ɓangaren, Farfesa Gusau ya ce manufar rubuta littafin shi ne don samar da tarihin Masauratun Hausa a littafi guda kasancewar kafin wannan lokaci babu makamancin littafin.

Kazalika, Gusau ya ce ƙarfafa haɗin kai a tsakanin Masarautun Hausa na daga cikin manufofin wallafa littafin.