Dattawan Arewa sun yi gargaɗi kan shirin kwashe jiragen yaƙi daga Zaria zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta yi gargaɗin shirin da ake zargin ana yi na kwashe wasu jiragen yaƙi daga Kwalejin Koyon Tuƙin Jirgin Sama, NCAT, da ke Zaria a Jihar Kaduna zuwa Jihar Legas.

Sanarwar da ta fitar ranar Lahadi ta hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a, Abdul-Azeez Suleiman, ƙungiyar ta ce jita-jitar da ake yaɗawa abin damuwa ne ainun musamman idan aka yi la’akari da daɗaɗɗen tarihin cibiyar da kuma rawar da take takawa ga cigaban fannin sufurin jiragen saman ƙasar nan.

Ƙungiyar ta yi ra’ayin “sake ma jiragen wuri na da mummunan sakamako ba ga cibiyar kaɗai ba har ma ga ilahirin fannin sufurin jiragin sama a ƙasa.

“Jiragen yaƙin da cibiyar ta NCAT za su yi matuƙar amfani ga ‘yan baya wajen daƙile buƙatun gaggawan da ka iya tasowa.

“Kwashe jiragen zuwa wani wuri da ba a sani ba zai saɓa wa ingancin horon da ake bai wa ɗalibai a kwalejin da kuma cikas ga tsaron fannin sufurin jiragin saman Nijeriya.”

Ta ƙara da cewa, wannan mataki abin a sake dubawa ne saboda irin illar da hakan zai haifar muddin aka aiwatar.

Sai dai kuma Ministan Sufurin Jirgin Sama na Nijeriya, Festus Keyamo, ya ce zargin ba gakiya ba ne.

Ya bayyana haka ne cikin sanarwar da ya fitar mai ɗauke da sa hannun kakakinsa, Tunde Moshood, yana mai bayyana rahoton a matsayin mara tushe balle makama.