An sulhunta tsakanin Gwamna Abba da Sheikh Daurawa

*Daurawa ya amince ya koma muƙaminsa na shugabancin Hisbah

Daga BASHIR ISAH

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya amince ya koma kan muƙaminsa a matsayin Kwamandan Hukumar Hisbah domin ci gaba daga inda ya tsaya.

Daurawa ya amince da hakan ne bayan da malamai suka shiga suka suhulta tsakaninsu da Gwamnan Kano, Abba Kabir.

Tun farko, Malam Daura ya sanar da ajiye muƙamin nasa cikin wani faifain bidiyo da aka yaɗa inda aka ji shi yana bai wa Gwamna Kabir haƙuri kana daga bisani ya ce ya ajiye shugabancin Hisbah.

Gwamna Kabir ya yi ƙorafi kan yadda hukumar ta Hisbah ke gudanar da aikinta inda ya ce jami’an hukumar kan kama matasa maza da mata suna jefawa a bayan mota kamar dabbobi, lamarin da ya ce bai kamata ba.

Sai dai wasu na ra’ayin cewa Gwamna Kabir ya soki aikin Hisbah ne saboda kama fitacciyar ‘yar TikTok ɗin nan ta Kano, wato Murja Kunya, wadda ta kasance ɗaya daga cikin masoyiyan Abba Kabir.

MANHAJA ta kalato an ga Malam Daurawa bisa rakiyar wasu malamai a Fadar Gwamnatin Kano a lokacin da suka je tattaunawa.

An ce Dr Said Ahmad Dukawa shi ne ya yi magana da ‘yan jaridu a madadin majalisar malaman inda ya ce Malam Daurawa zai koma bakin aiki.

Waɗanda suka halarci zaman sulhun sun haɗa Farfesa Musa Borodo da Farfesa Salisu Shehu da sauransu.