Gwamnatin Zamfara ta tantace tsoffin ma’aikata 3079, ta biya bashin giraduti na N2.3bn

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta samu nasarar tantance ma’aikatan jihar da suka yi ritaya 3,079 a ƙoƙarin da take yi na ganin ta warware bashin giradutin da ake bin gwamnatocin da suka gabata.

Rabon tsoffin ma’aikatan jihar da samun haƙƙinsu na giraduti tun a shekarar 2011, kamar yadda sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris ta nuna.

Sulaiman ya ce kawo yanzu an biya masu karɓar fansho a matakin jiha da ƙananan hukumomi su 1746 kuɗi N2,312,841,065.08.

Ya ce a Juma’ar da ta gabata aka fara biyan kashi na biyu na masu karɓar fansho haƙƙinsu na giraduti, wanda a cewarsa, hakan ya samar da walwala a gare su.

Ya ƙara da cewa, “An samu cigaba sosai game da tantance masu karɓar fansho a matakin jiha da ƙananan hukumomi. Kuma an fara biyan kashi na biyu na masu karɓar fansho giraduti a ranar Juma’a, 1 ga Maris, 2024.

“Mutum 413 da aka tantance a matakin jiha an biya su kimanin Naira Miliyan 682.2.

“Haka nan, kashi na biyu na waɗanda aka tantance a matakin ƙananan hukumomi su 403, an biya su Naira miliyan 449.6.

“Sannan mutum 1746 daga cikin 3079 da aka tantance a matakin jiha da ƙananan hukumomi, an biya su giraduti a cikin kashi biyu. Abin da aka biya kawo yanzu ya kama biliyan N2,312,841,065.08.

“Kumar har yanzu shirin tantancewa na cigaba da gudana inda akan biya waɗanda aka kammala tantance su ɗin haƙƙoƙinsu,” in ji sanarwar.

By Editor